'Ka Daina Tsoma Baki a Harkokin Arewa': An Yi Jan Kunne ga Shettima kan Kalamansa
- Kungiyar 'Arewa Ina Mafita' ta soki Yerima Shettima kan tsoma baki a harkokin yankin Arewa duk da cewa daga jihar Lagos ya fito
- Shugaban kungiyar, Kwamred Nura Hussaini, ya ce Shettima yana amfani da sunan Arewa don biyan bukatunsa, ba don kishin yankin ba
- Kungiyar ta zargi Shettima da cin mutuncin Nasir El-Rufai da wasu ‘yan Arewa domin samun kusanci da Gwamna Uba Sani da samun kwangiloli
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kungiyar matasa ta Arewa Ina Mafita ta yi martani ga shugaban matasan Arewa (AYCF), Yerima Shettima kan kalaman da yake yi a Arewa.
Kungiyar ta gargadi Shettima kan tsoma baki a lamuran Arewa duba da cewa daga jihar Lagos ya fito.

Source: Facebook
Arewa: Matasa sun taso Yerima Shettima a gaba
Shugaban kungiyar, Kwamred Nura Hussaini shi tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Juma'a.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito: Rundunar tsaro ta faɗi wadanda ke kai hare hare a jihohin Arewa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Abin ya zama dole a fadi gaskiya, koda kuwa ba za ta yi dadi ba, Yerima Shettima, kai da kanka kasan cewa kai ba ɗan Arewa ba ne.
"Ka fito ne daga jihar Lagos a Kudu maso Yammacin Najeriya, ba ka da komai da ya hada ka da Arewa, al'adunta da dabi'arka.
"Salon rayuwarka da komai na ka duk sun sabawa tsarin mutanenmu na Arewa."
Kungiyar ta ce abin mamaki da takaici ne a ce Shettima na fakewa da sunan 'kungiyar Arewa' wajen biyan bukatunsa.
Ta ce:
"Amma abin mamaki da takaici, shi ne yadda kake fakewa da sunan 'kungiyar Arewa' wajen biyan bukatunka na kashin kai.
"Kana fitowa ka tsoma baki cikin harkokin Arewa tamkar wani jagoran yankin, alhali kai ba ka da tushen da zai ba ka wannan damar.
"Ya dace ka dawo hankalinka ka bar al’umma su tafiyar da kansu da ikon su."

Source: Original
An soki Yerima Shettima kan El-Rufai
Matasan sun koka kan yadda Shettima ya dura kan Malam Nasir El-Rufai da wasu fitattun yan Arewa saboda neman gindin zama a wurin Gwamna Uba Sani.
Ya kara da cewa:
"Yanzu kuma ka fara sukar Malam Nasiru El-Rufai da wasu fitattun 'yan Arewa domin kawai ka samu kusanci da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna don samun na abinci da kwangila.
"Wannan siyasar da ka ke yi da sunan Arewa jama’a sun gaji da ita, ai ba don kishin Arewa kake magana ba, domin da haka ne da tun da farko ka rika magana a kan matsalolin tsaro, yunwa, rashin aikin yi da talaucin da ke addabar mutanen Arewa.
"Amma me ya sa ba ka ce uffan a kan wadannan ba? Ko dan hakan ba zai faranta ran masu mulki ba?"
Kungiyar ta ce Arewa ba ta bukatar masu yaudara tare da kwadayin mulki, masu amfani da sunanta don gina kansu.

Kara karanta wannan
Daga hawa karaga, Gwamna ya sa an cafke Sarki da fadawansa kan naɗa kansa a sarauta
Ta ce idan yana da kishin Arewa, me ya sa bai taba taka rawa wajen kare martabarta ba face sukar wasu da sunan gyara?
Ta kara da cewa duk wanda ya san Yerima Shettima ya san cewa amfani yake da sunan "Arewa" a matsayin hanya ta samun kudi da mukami.
Kungiyar matasa ta caccaki masu sukar Tinubu
Kun ji cewa wata kungiyar matasan Arewa ta AYCF, ta yi martani mai zafi ga ƴan siyasar yankin masu sukar gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kungiyar, Yerima Shettima ya bayyana cewa ƴan siyasar suna yi ne kawai don sun kasa samun muƙami a gwamnatin.
Shettima ya dura kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai inda ya ce bai kamata yana magana da yawun Arewa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
