‘Yan Kudu maso Gabas ba su shirya mulkin Najeriya ba – Inji Shettima Yerima
Shettima Yerima, wanda shi ne shugaban kungiyar Matasan Arewa ta AYCF, ya ce Yankin Kudu maso Gabashin Najeriya bai shirya karbar mulkin kasar nan a 2023 ba.
Alhaji Shettima Yerima, ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi hira da Jaridar Vanguard. Yerima ya ke cewa Yankin Kudancin kasar na yi wa Najeriya barazana.
A na sa ra’ayin, Kudu maso Gabas ba za su fito da shugaban kasa a zabe mai zuwa ba saboda mutanen Yankin sun kyale ‘Ya ‘yansu su na ta faman kiran raba kan kasa.
Shugaban kungiyar Matasan a karkashin AYCF ya ke cewa babu yadda za ayi 'Dan Ibo ya zama shugaban kasa a lokacin da wasunsu ke kiran a barka Najeriya gaba daya.
Yarima yake cewa: “Ba za ku cigaba da yi wa zaman lafiyan kasar nan barazana ba, domin lokaci ya yi da ba za su ku nemi mulki da barazana ba, ku na bukatar ku kama-kafa.”
“Ba zai yi yiwu ku kalli kwayan idanunmu ku ci wa ‘Yan Najeriya mutunci, ku raina hankalin gwamnati ba, sannan ku ce ana tsoronku. Wa ke tsoronku?” Ya tambaya!
Yerima ya yi kira ga Yankin Kudu na Gabas da su ja-kunnen Mutanensu, su kuma rika siyasa ba tare da yunkurin kiran a raba kasa ba ko yi wa ‘Yan Najeriya barazana ba.
Kamar yadda Jaridar ta bayyana, Yarima Shettima ya nuna cewa idan har Ibo su ka nemi a zauna lafiya, to ta haka ne za su samu mulkin Najeriya cikin sauki a zabe na gaba.
A wasu rahotannin, gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya fito ya na cewa burin da wasu su ke da shi na tsayawa takara a zaben 2023 ba zai wargaza APC a 2023 ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng