Bayan Mutuwar Francis, an Zaɓi Sabon Fafaroma da Zai Jagoranci Kiristocin Duniya
- An zaɓi Robert Francis Prevost daga Amurka a matsayin sabon Fafaroma, wanda zai jagoranci cocin Katolika bayan rasuwar Fafaroma Francis
- Zaɓen Prevost ya kawo gagarumin sauyi a tarihin cocin Katolika, yayin da Amurkawa ke murnar ganin ɗan ƙasarsu ya zama Fafaroma
- Yanzu haka, Fafaroma Prevost zai fara sabuwar rawar da zai taka wajen kula da miliyoyin mabiya Katolika da ke sassa daban-daban na duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rome, Italy - Bayan mutuwar Fafaroma Francis a ranar 21 ga watan Afrilun 2025, an zabi sabon shugaban katolika.
Fadar katolika ta shiga dakin zaben sabon Fafaroma a yau Alhamis 8 ga watan Mayun 2023.

Source: UGC
An zaɓi sabon Fafaroma na cocin katolika
Rahoton Al Jazeera ya tabbatar da haka inda ya ce an zabi Fafaroma a yau Alhamis fiye da mako 2 bayan mutuwar tsohon shugaban cocin katolika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan daukar dogon lokaci ana zaben sabon shugaban, an sanar da Robert Francis Prevost a matsayin sabon Fafaroma.
Prevost, wanda ya fito daga Amurka, ya karɓi ragamar shugabancin cocin Katolika daga hannun marigayi Francis.
Sanarwar ta zo a matsayin babban sauyi a tarihin cocin Katolika, inda Amurkawa ke nuna farin ciki da alfahari da samun nasarar ɗan ƙasarsu.
Ya gaji Fafaroma Francis, wanda ya rasu watan da ya gabata yana da shekaru 88, bayan fiye da shekara goma yana jagorantar mabiya Katolika a duniya.
Wanene sabon Fafaroma Robert Francis Prevost?
Paparoma Leone XIV, wanda aka haifa da suna Robert Prevost, dan asalin Amurka ne, yana da gogewa sosai a aikin coci, musamman ta hanyar aikin da'awa da ya yi a Peru.
Ya iya harshen Sifaniyanci sosai, kuma yana da kwarewa wajen jagoranci da kulawa ta bangaren addini.
Fafaroma Francis ne ya nada shi shugaba a ofishin da ke da alhakin nadin bishop a Vatican, wani matsayi mai matukar muhimmanci da ke tsara shugabannin cocin Katolika a duniya.

Source: UGC
Sabon Fafaroma zai ci gaba daga inda aka tsaya
Zabensa ya zama wata babbar alama ga Katolikan Amurka da ma cocin Katolika ta duniya baki daya, domin yana iya ci gaba da aikin Francis na coci mai karbar kowa da tausayi.
Kardinal Robert Francis Prevost ya sadaukar da rayuwarsa ga bautar Allah, aiki a kasa da kasa, da biyayya maras yankewa ga kiran coci.
An haife shi a Chicago a 1955, ya taso a gida da limamai ke yawan ziyarta, saboda darajar mahaifiyarsa ‘yar Sifen, Mildred Martínez.
Mahaifinsa, Louis Marius Prevost, wanda dan Faransa da Italiya ne, ya kasance mai koyar da addini, Robert ya taso yana mai hidima a coci tun yana yaro.
Daga karshe, ya zabi tsarin Augustinian saboda tsarin hadin kai da koyarwar St. Augustine na Hippo, CNN ta ruwaito.
Fasto ya fadi sanadin mutuwar Fafaroma
Kun ji cewa wani Fasto a Najeriya ya nuna takaici bayan rasuwar Fafaroma Francis a ƙarshen watan Afrilun 2025.
Fasto Chris Oyakhilome ya ce allurar rigakafin COVID-19 ce ta kashe Fafaroma Francis, yana danganta mutuwarsa da hadin kai da masu mulki.
Oyakhilome ya soki Fafaroma saboda goyon bayan rigakafin, yana cewa lafiyarsa ta tabarbare bayan karɓar allura.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


