'Yan Bindiga Sun Zo Kwatar Abokinsu, Sojoji Sun Hallaka Hatsabibin Ɗan Ta'adda
- Sojojin Operation FANSAN YANMA sun hallaka wani shahararren shugaban ’yan bindiga a jihar Katsina da ke fuskantar matsalar tsaro
- Marigayin mai suna Abubakar da aka fi sani da Mallam da ke garin Danmusa ya rasa ransa bayan artabu da jami'an tsaro a Katsina
- Jami’an tsaro sun bazama bincike a jeji da kauyuka domin kama wadanda suka tsere da kuma rushe sansanonin 'yan ta'adda gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Dakarun sojoji na ci gaba da samun galaba kan hatsabiban yan bindiga da suka addabi al'umma a jihar Katsina.
A yan kwanakin nan, rundunar sojoji na ci gaba da samun nasarar hallaka manyan hatsabiban yan bindiga.

Source: Original
Ƙoƙarin sojoji kan yan bindiga a jihohin Arewa
Rahoton Zagazola Makama ya ce an yi nasarar hallaka riƙakken ɗan ta'adda, Mallam a ranar 5 ga watan Mayun 2025 da dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mafi yawan inda aka fi samun nasara kan yan bindiga a Arewa maso Yamma ne musamman jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina.
Al'ummar yankuna da dama na korafi duba da yawaitar hare-haren yan bindiga wanda ke jawo asarar rayukan mutane da rasa dukiyoyi.
Sai dai dakarun sojoji na kokari musamman ganin yadda suke yi wa manyan yan bindiga dauki daidai a mabambantan hare-hare.
Katsina: Sojoji sun hallaka ɗan bindiga, Mallam
Sojojin Operation FANSAN YANMA sun hallaka dan bindigan yayin wani yunkuri da ’yan ta'adda suka yi domin kubutar da abokinsu a Danmusa a Jihar Katsina.
Hakan ya faru ne lokacin da ’yan bindigar suka kai hari domin kubutar da Kamalu Buzare, wanda jami’an tsaro suka kama a baya.
Bayan samun bayanan sirri kan ’yan ta’addan, tawagar sojoji, ’yan sanda da jami’an tsaron al’umma suka tunkari harin domin fatattakar su.

Source: Twitter
Yadda aka hallaka ɗan bindiga a Katsina
A cewar majiyoyin soja, karfin wutar da dakarun suka yi amfani da shi ya rinjayi ’yan bindigar, wanda hakan ya sa suka gudu.
Majiyar ta ce:
“A yayin farautarsu, wani rikakken dan bindiga mai suna Abubakar wanda aka fi sani da Mallam, ya rasa ransa.
"An gano gawarsa a wajen garin Danmusa da misalin karfe 2:50 na rana a ranar 6 ga watan Mayu 2025."
Sojoji sun kara zurfafa bincike a yankunan da ke makwabtaka da dazuka domin cafke wadanda suka tsere da kuma rusa sansanoninsu gaba daya.
Dakarun Operation FANSAN YANMA na ci gaba da matsa wa bata-gari lamba a jihar Katsina da sauran yankin Arewa maso Yamma domin dawo da zaman lafiya.
Sojoji sun yi ajalin dan bindiga a Katsina
A baya kun ji cewa wani hatsabibi kuma jagoran 'yan bindiga, Harisu Babba Yauni wanda ya mutu tare da wasu daga cikin yaransa a rikicin cikin gida da ya auku a dajin Yauni.
An ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar 23 ga Afrilu, 2025, a karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina, a cewar jami'an tsaro.
Rahotanni sun an gano cewa wasu gungun 'yan bindiga daga Kambarau, Tudun Dole da dajin Mahuta suka kai masa farmaki suka hallaka shi da mabiyansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

