'Yan Bindiga Sun kai Hari Mai Zafi Filato, Sun Afkawa Mutane Suna Barci

'Yan Bindiga Sun kai Hari Mai Zafi Filato, Sun Afkawa Mutane Suna Barci

  • Akalla mutane shida sun rasa rayukansu a wani hari da 'yan bindiga suka kai Marit da Gashish a karamar hukumar Barkin Ladi a Filato
  • Harin ya faru ne a daren Litinin lokacin da mazauna yankin ke barci, lamarin da yake kara nuna raunin jami'ai da hukumomin tsaro na kasa
  • Shugaban karamar hukumar, Hon. Stephen Pwajok Gyang, ya tabbatar da harin, yana mai cewa an riga an yi jana’izar wadanda suka mutu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Akalla mutane shida aka kashe a wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai kauyukan Marit da Gashish da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Har ila yau, a sakamakon harin an samu wasu da dama da suka jikkata kuma aka garzaya da su asibiti.

Kara karanta wannan

Matashi ya kashe mahaifinsa bayan sassara wuyansa da adda a Jigawa

Filato
'Yan bindiga sun kai sabon hari Filato. Hoto: The Government of Plateau State
Source: Twitter

Wani dan yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa harin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na dare lokacin da mutane ke barci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban karamar hukumar Barkin Ladi, Hon. Stephen Pwajok Gyang, ya tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawunsa, Mercy Yop Chuwang.

Hon. Stephen Pwajok Gyang ya bayyana cewa an yi jana’izar wadanda suka mutu a ranar Litinin da harin ya faru.

Mutane sun jikkata a sabon harin Filato

Pwajok ya ziyarci wadanda suka jikkata a babban asibitin Barkin Ladi inda ya nuna alhini bisa sake tasowar rikici a yankin, musamman a lokacin da ake kokarin tabbatar da zaman lafiya.

Ya yaba da kokarin jami’an tsaro da na sa-kai wajen dakile matsalolin, amma ya bukace su da su kara zage damtse domin hana sake aukuwar irin wannan hari a gaba.

The Nation ta rahoto cewa Stephen Pwajok Gyang ya ce:

Kara karanta wannan

Turji ya zafafa hare-hare a Sakkwato, mazauna kauyuka 20 sun fara kaura

“Dole ne a kawo karshen kashe kashe.
"Ina kira ga hukumomin tsaro, shugabannin al’umma da mazauna yankin da su hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Ana jiran karin bayani daga hukumomi

Rahoton ya bayyana cewa hukumomin tsaro, ciki har da Operation Safe Haven da rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba a lokacin hada wannan rahoto.

Wannan hari na Marit da Gashish ya zo ne bayan makonni biyu da hare-hare makamanta su suka hallaka mutane fiye da 100 a yankunan Bokkos da Bassa.

Baya ga hare haren, ana ci gaba da samun rahotannin harbin shanu da zargin saka musu guba a Bassa, Riyom da Mangu.

Yan sanda
Ana jiran bayani wajen 'yan sanda kan harin da aka kai Filato. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Stephen Pwajok ya yi addu’ar Allah ya ba iyalan mamatan da al’ummomin da abin ya shafa hakuri da kwanciyar hankali, tare da bukatar hanzarta kula da lafiyar wadanda suka jikkata.

An kama mai kashe kashe a jihar Filato

Kara karanta wannan

Wike ya zargi gwamna Fubara da jawo wulakanta matar Tinubu a Rivers

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta kama wani matashi da ake zargi yana da hannu a kashe kashe da ake a Filato.

An kama matashin ne a lokacin da yake kokarin shiga jihar Taraba a karamar hukumar Shongom ta jihar Gombe.

Rahoton 'yan sanda ya nuna cewa an dauki matashin ne haya domin ya taya wani mutum fada da bindiga a wani yanki na jihar Filato.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng