'Yan Karota zasu fara kamen baburan adaidaita a jihar Kano

'Yan Karota zasu fara kamen baburan adaidaita a jihar Kano

- Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano ta ce duk direban adaidaita da ya hau titi babu sabuwar lamba a ranar Alhamis zai fuskanci fushin hukumar

- Shugaban hukumar, Baffa Babba Danagundi ne ya tabbatar da hakan da a wani taron manema labarai da hukumar ta kira

- Ya ce hukumar KAROTA ta kammala sanya na’urar ta Tracker a jikin baburan adaidaita sahu kuma za ta fara bawa direbobin suka yi sabuwar lambar

Hukumar kula da zirga-zairgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce a yau Alhamis dinnan, duk wani direban babur din adaidaita da ya hau kan titin jihar ba tare da sabuwar lambar da hukumar ta ba da ba, zai fuskanci fushin hukumar.

Shugaban hukumar, Baffa Babba Danagundi ne ya bayyana haka ga manema labarai a yammacin ranar Talata a wajen taron da hukumar ta kira na manema labarai, hukumar ta kira wannan taro ne don kaddamar da fara sanya na’urar da za ta dinga gano inda ababen hawa suke.

'Yan Karota zasu fara kamen baburan adaidaita a jihar Kano
'Yan Karota zasu fara kamen baburan adaidaita a jihar Kano
Asali: Twitter

Shugaban ya ce hukumar ta gama sanyawa baburan adaidaita din na’urar Tracker za kuma ta fara bai wa direbobin da suke da sabuwar lamba a yau Alhamis din nan tare da bada katin shaidar yin rijista, wato ID card.

KU KARANTA: Cristiano ya bar tarihi a duniya, yayin da ya zama mutum na farko da yafi kowa mabiya a Instagram a duniya

Idan za a tuna, a ranar Litinin ne jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, KAROTA a jihar Kano za ta fara kwace ababen hawa marasa rijista a jihar daga ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu.

Manajan daraktan KAROTA, Alhaji Baffa Dan agundi ya sanar da hakan a ranar Litinin tare da tabbatar da cewa za a rufe yi wa adaidaita sahu rijista a jihar a daren Laraba.

Kamar yadda takardar da kakakin cibiyar, Nabilusi Abubakar Kofar Na'isa ya fitar kuma jaridar Solacebase ta samu, ta ce an yanke wannan shawarar ne a ranar Litinin bayan taron da shugabannin kungiyoyin 'yan adaidaita suka yi a jihar.

Sai dai kuma wasu suna tsokaci akan cewa wannan hanya da gwamnatin jihar ta dauko ta kwacewa mutane ababen hawa ba za ta haifar da da mai ido ba.

Duba da yadda ta'addanci yayi katutu a kasar, wanda ke da nasaba da rashin aikin yi, mutane na ganin cewa duk wanda aka kwacewa abin hawa ya rasa sana'ar yi zai iya fara aikata abubuwa wanda basu dace ba, wanda hakan ba abu ne mai kyau ga jihar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel