Mutane Miliyan 2 Sun Kamu da HIV a Najeriya, An Ji Jihohi 3 da abin Ya Fi Shafa
- Rahoton NACA na 2024 ya bayyana cewa jihar Rivers ce ke da mafi yawan masu HIV da adadin mutane 208,767, sai Benue da Akwa Ibom
- Mutane sama da miliyan biyu ke dauke da HIV a Najeriya, lamarin da ke bukatar karin wayar da kai, gwaji da samun magani cikin sauki
- Abuja, sannan Legas, Anambra na daga cikin wuraren da ke da yawan masu HIV, inda jihar Kano ke da mutane 53,972 masu dauke da cutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahoton shekarar 2024 da Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa (NACA) ta fitar ya bayyana cewa jihar Rivers ce ke da mafi yawan masu dauke da cutar HIV a Najeriya.
Adadin masu dauke da HIV a Rivers ya kai mutane 208,767, yayin da Benue ke biye da ita da mutane 202,346 sai kuma Akwa Ibom da mutane 161,597.

Kara karanta wannan
'Ya na da kirki': Tsohon gwamna ya fadi kyautar da Marigayi Fafaroma ya taba ba shi

Source: Getty Images
Sama da mutane miliyan 2 ke dauke da HIV
Wadannan jihohi uku ne ke saman jerin jihohin da suka fi yaduwar cutar a sababbin alkaluman da aka fitar daga shirin kididdigar HIV na kasa, inji Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jimillar masu fama da cutar a fadin Najeriya ya haura miliyan biyu, lamarin da ke kara nuna bukatar wayar da kai, gwaji da kuma samun maganin HIV cikin sauki.
Jihar Legas wadda ke matsayin cibiyar kasuwancin Najeriya, na da mutane 108,649 da ke dauke da HIV, yayin da Anambra ke da mutane 100,429.
A Abuja, an ce mutane 83,333 ne suka kamu da cutar, lamarin da ya sa birnin ya zama daya daga cikin masu yawan masu dauke da HIV a Arewa ta Tsakiya.
Adadin masu dauke da HIV a sauran jihohi
Jihohi masu yawan adadin masu dauke da HIV:
- Delta – 68,170
- Imo – 67,944
- Enugu – 61,028
- Edo – 60,095
- Taraba – 58,460
Jihohi masu matsakaicin yawan cutar:
- Abia – 54,655
- Kaduna – 54,458
- Kano – 53,972
- Plateau – 51,736
- Borno – 50,433
- Oyo – 50,063
- Nasarawa – 44,993
- Cross River – 43,452
- Ogun – 43,348
Jihohi da ke da karancin adadi:
- Adamawa – 40,059
- Gombe – 31,825
- Jigawa – 31,409
- Osun – 30,714
- Niger – 29,756
- Bauchi – 28,698
- Kogi – 28,421
- Ondo – 27,150
- Katsina – 26,788
- Bayelsa – 25,339
Jihohi mafi kankantar yaduwar cutar:
- Kwara – 20,259
- Kebbi – 19,339
- Ekiti – 18,857
- Sokoto – 15,223
- Ebonyi – 14,151
- Zamfara – 13,253
- Yobe – 11,956

Source: Getty Images
Mutane 43,683 sun mutu daga HIV a 2024
Rahoton ya kara da cewa 43,683 sun mutu sakamakon cutar a bara, inda aka ce manyan mutane 28,589 ne suka mutu (maza 13,650, mata 14,939).
Sannan ya kuma ce adadin yara ‘yan kasa da shekara 15 da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar HIV a 2024 ya kai 15,094, inji rahoton Business Hallmark.
A halin yanzu, 1,753,425 daga cikin masu cutar HIV sun san matsayinsu, ciki har da manya 1,693,457 (maza 579,209, mata 1,114,401) da yara 54,983 masu shekaru 0 zuwa 14.
Tinubu ya dauki mataki kan yaki da HIV
A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar zartarwa ta amince da Naira biliyan 4.5 don siyan magungunan HIV ga masu fama da cutar a fadin Najeriya.
Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate, ya bayyana cewa shirin zai tabbatar da wadatar magunguna ga masu dauke da HIV ba tare da tangarda ba.
FEC ta kafa kwamitin hadin gwiwa daga ma’aikatun gwamnati daban-daban domin tsara ingantaccen tsarin kula da lafiyar jama’a mai dorewa.
Asali: Legit.ng

