Sabon rahoto: Yan Nigeria Miliyan 2 ne ka karbar maganin cutar HIV - NACA

Sabon rahoto: Yan Nigeria Miliyan 2 ne ka karbar maganin cutar HIV - NACA

- Hukumar dakile kamuwa da yaduwar cuta mai karya garkuwar dan Adam, NACA, ta ce akalla 'yan Nigeria 1,090,233 ke karbar maganin garkuwa daga cutar

- Mr Ashefor ya ce, shirin tallafi na shugaban kasar Amurka ya taimaka da kusan kaso 75 zuwa 80 na magance cutar yayin da asusun GF ya taimaka da wajen kaso 20

- Mukaddashin daraktan ya ce gwamnatin tarayya na shirin kara mutane 50,000 daga jihohin Taraba da Abia a cikin wadanda za su ci gajiyar wannan tallafi na maganin cutar

Hukumar dakile kamuwa da yaduwar cuta mai karya garkuwar dan Adam, NACA, ta ce akalla 'yan Nigeria 1,090,233 ke karbar maganin garkuwa daga cutar, bisa rahoton da ta tattara a watan Yunin wannan shekarar.

Mukaddashin daraktan sashen bincike, sa ido da kuma tantancewa na hukumar NACA, Gregoary Ashefor, ya bayyana hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Alhami, a Legas.

Ya yi jawabi ne a wani taron horaswa da ma'aikatar lafiya ta kasa NACA da kuma asusun Global Fund, suka dauki nauyin gudanarwa don horas da ma'aikatan fannin sanin makamar aiki kan alkinta bayanan kiwon lafiya da kuma tsarin dorewar tsare tsaren kiwon lafiya musamman a dakunan gwaje gwaje.

KARANTA WANNAN: Da zafi zafi: Buhari ya kaddamar da dokar ta baci akan tsafta da samar da ruwa a Nigeria

Sabon rahoto: Yan Nigeria Miliyan 2 ne ka karbar maganin cutar HIV - NACA

Sabon rahoto: Yan Nigeria Miliyan 2 ne ka karbar maganin cutar HIV - NACA
Source: Original

Mr Ashefor ya ce, shirin tallafi na shugaban kasar Amurka kan garkuwa daga cutar AIDs ya taimaka da kusan kaso 75 zuwa 80 na magance cutar yayin da asusun GF ya taimaka da wajen kaso 20.

Mukaddashin daraktan ya ce gwamnatin tarayya na shirin kara mutane 50,000 daga jihohin Taraba da Abia a cikin wadanda za su ci gajiyar wannan tallafi na maganin cutar. A cewarsa, a yanzu haka, akwai mutane 76,000 ke samun magungunan a Taraba da Abia, kuma gwamnati ce ke daukar nauyi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel