MURIC Ta Tono Wata Jami'a a Najeriya da Ake Tilasta wa Ɗalibai Musulmai Zuwa Coci
- Kungiyar MURIC ta zargi jami’ar Adeleke da hana dalibai Musulmi gudanar da ibadun Ramadan, ana tilasta musu halartar cocin makarantar
- MURIC ta ce jami’ar ta katse sallar tarawihi da dalibai suka gudanar, tare da gargaɗinsu da kada su sake yin hakan a harabar makarantar
- Kungiyar ta bukaci NUC da ta binciki dokokin jami’ar, tana mai cewa an haramta sallah da sanya hijabi, kuma ana tauye ‘yancin dalibai Musulmi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Kungiyar kare haƙƙin Musulmi (MURIC), ta zargi jami’ar Adeleke da ke Ede, jihar Osun, da hana dalibai Musulmi gudanar da ibadun Ramadan.
Babban daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, yana mai cewa jami’ar ta na tilasta wa dalibai Musulmi halartar shirye-shiryen cocin jami’ar.

Asali: Twitter
'Ana tilasta daliban jami'a zuwa coci' - MURIC
A sanarwar da ta fitar a shafinta na intanet, MURIC ta ce ta samu koke da dama daga dalibai Musulmi da ke jami’ar, suke cewa an hana su gudanar da ibada, musamman a watan Ramadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, an ji jami’ar na amfani da hanyoyi daban-daban don hana dalibai Musulmi gudanar da addininsu, ciki har da wajabta halartar coci.
An kuma zargi jami’ar da katse sallar tarawih da daliban suka yi kwanaki biyu da suka gabata, tare da yi musu gargaɗi da kada su sake yin hakan.
MURIC ta bayyana wannan matakin jami’ar a matsayin rashin mutunta addinin Musulunci, tana mai cewa hakan wani yunkuri ne na tauye ‘yancin dalibai Musulmi.
MURIC ta shigar da korafi kan jami'ar Adeleke
Farfesa Akintola ya ce tun a shekarar 2019 MURIC ta gabatar da irin waɗannan zarge-zarge a kan Jami’ar Adeleke, inda ta bukaci hukumar kula da jami’o’i (NUC) da ta binciki batun.
A cewarsa, jami’ar na ci gaba da tauye wa dalibai Musulmi ‘yancinsu ta hanyar tilasta musu halartar cocin jami’a a ranakun Lahadi, Laraba da Asabar.
MURIC ta ce an haramta duk wata ibadar Musulunci a harabar jami’ar, ciki har da yin Sallah, yayin da sanya hijabi ke daga cikin abubuwan da ba a yarda da su ba.
Akintola ya ce jami’ar tana ɓoye waɗannan dokoki daga dalibai har sai sun biya kuɗin makaranta, sannan su gano cewa ana tauye musu ‘yancin addini.
MURIC ta nemi NUC ta binciki jami'ar Adeleke

Asali: Twitter
MURIC ta bukaci NUC da ta duba littafin dokokin daliban jami’ar, musamman shafi na 7, 49, 50, 56 da 60, waɗanda ke da dokokin da ke tauye ‘yancin dalibai Musulmi.
Kungiyar ta bukaci NUC da ta gaggauta ɗaukar mataki domin kare ‘yancin dalibai Musulmi da ke karatu a jami’o’in da ke cikin ƙasar nan.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun kama matasa da bindigogi 10, harsasai 124 za su kai wa ƴan ta'adda
Farfesa Akintola ya ce:
"Ba Jami’ar Adeleke kaɗai ba, yawancin jami’o’in kudi na yankin Kudu na aiwatar da irin waɗannan munanan ayyuka."
MURIC ta bayyana damuwa kan yadda hukumomi ke yin shiru kan irin waɗannan zarge-zarge, duk da cewa akwai hujjojin da ke nuna ana tauye ‘yancin addini.
Kungiyar ta bukaci jami’an gwamnati da su yi abin da ya dace don tabbatar da adalci ga dalibai Musulmi da ke fama da irin wannan matsala.
Kotu ta amincewa dalibai mata hijabi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bayan shari’ar shekaru shida, kotu ta yanke hukunci kan batun ‘yancin ɗalibai mata Musulmai na sanya hijabi a makaranta.
Kotun ta amince da cewa ɗalibai mata Musulmai a makarantar sakandare ta 'International School' da ke cikin Jami’ar Ibadan na da ‘yancin dora hijabi a saman kayan makaranta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng