MURIC Ta Fada Wa Musulmi Su Ƙauracewa Wasu Jami'o'in Kirista Saboda Hana Amfani Da Hijabi Da Wasu Dalilai

MURIC Ta Fada Wa Musulmi Su Ƙauracewa Wasu Jami'o'in Kirista Saboda Hana Amfani Da Hijabi Da Wasu Dalilai

  • Farfesa Ishaq Akintola, shugaban kungiyar kare hakkin musulmi MURIC ya shawarci musulmin Najeriya su guji jami'o'i masu zaman kansu mallakin kiristoci
  • Shugaban na MURIC ya ce ya samu korafe-korafe da dama da ke nuna ana hana musulmi saka hijabi, ana tilasta musu halarton tarukan kiristanci da wasu abubuwan na tsangwama
  • Ishaq ya shawarci iyayen dalibai su rika yin bincike sosai kafin saka 'ya'yansu a jami'o'in har zuwa lokacin da masu jami'o'in za su gyara halayensu ko NUC ta dauki mataki kansu

Kungiyar kare hakkin musulunci MURIC ta fada wa musulmin Najeriya su kauracewa dukkan jami'o'i masu zaman kansu na kiristoci saboda rashin kyalle amfani da hijabi da wasu dalilai da kungiyar ta bayyana a matsayin 'adawa da musulunci'.

Farfesa Ishaq, shugaban MURIC ne ya yi wannan kiran cikin sanarwar da aka fitar a shafin kungiyar a ranar Alhamis, inda ya ce ya samu korafi masu yawa daga dalibai musulmai da ke karatu a kwallejojin kirista kan yadda ake tilastasu zuwa coci da yin wasu abubuwa da musulunci ya hana.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

MURIC
Kungiyar Musulunci, MURIC Ta Fada Wa Musulmai Su Kauracewa Wasu Jami'o'in Kirista Saboda Hana Amfani Da Hijabi. Hoto: SaharaReporters.
Asali: Facebook

Yadda jami'o'in Kirista masu zaman kansu ke tauye hakkin dalibai musulmi - MURIC

Sahara Reporters ta rahoto cewa ya kuma zargi mammalaka jami'o'in kiristoci da nuna kiyayya ga addinin musulunci da satar suna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Mun samu rahotanni daga dalibai musulmai da ke jami'o'i masu zaman kansu mallakar kiristoci dangane da kiyayyar musulunci. Ba a kyalle dalibai musulmi su yi addininsu a wadannan jami'o'i masu zaman kansu. Ba za su iya kafa kungiyoyin dalibai musulmi ba.
"Kuma, ba a basu wurin da za su yi sallah. Hijab haramun ne a irin wannan kasashen. Ana tilasta dalibai musulmi zuwa cocin kiristoci idan ake kiran rajista ake hukunta wadanda ba su tafi ba. Wadannan makarantun ba su kiyayye hakokin bil adama. Laifi ne idan kiristoci masu makarantu za su hana dalibai mata musulmi saka hijabi hakan yasa ana musu kallon kirista.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Kara Karfi a Arewa, Jiga-Jigai da Wasu Yan Takarar Majalisa Sun Koma APC

"Hakan zalunci ne, ya saba doka da kundin tsarin mulki. Barazana ne ga musulunci. Hakan hujja ne da ke nuna kiyayya ga addini da masu jami'o'in kirista ke yi."

Iyaye da dalibai su rika bincike sosai kafin shiga jami'o'i - MURIC

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Mafita ga musulmi shine iyayen dalibai su rika bincike sosai kafin su saka yayansu a jami'o'i masu zaman kansu a kasar. Su kuma guje wa wadanda kiristoci ne suka mallake su domin ba komai bane sai tarko na raba musulmi da addinansu."

Don haka MURIC ta yi kira ga dalibai musulmi da iyayensu su guje wa jami'o'in kiristoci masu zaman kansu har zuwa lokacin da hukumar kula da jami'o'i NUC za ta tsaftace su ko kuma su masu jami'o'in sun dena tsangwar addini su yi rayuwarsu su kyale kowa ya yi nasa.

MURIC Ta Nemi A Dauke Cibiyoyin JAMB, WAEC Daga Cocunan RCCG

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin wasu jihohi 5 na APC da Tinubu zai iya rasa kuri'unsu badi

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC ta bukaci hukumomin jarrabawar na JAMB da WAEC su dauke cibiyoyinsu daga cocin RCCG da ke babbar hanyar Legas-Ibadan.

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, Shugaban MURIC, Ishaq Akintola ya bayyana bukatar dauke cibiyoyin ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 26 ga watan Oktoban 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel