Watan Ramadan: Abubuwan da ya kamata a maida hankali a kai

Watan Ramadan: Abubuwan da ya kamata a maida hankali a kai

A halin yanzu an shiga kwanaki 10 na karshen watan azumin Ramadan mai alfarma. Ko a cikin watan dai wadannan kwanaki sun fi daraja da falala don haka aka so a maida hankali na musamman a cikin su domin samun dacewa.

Ga wasu ibadu nan da ake so a maida hankali a kan su:

1. Sallar dare

A cikin wadannan kwanaki na karshe ne ake samun daren da ake kira “Laylatul Qadr” wanda darajar sa ta fi ta daren watanni 1000. Tsayuwar dare a wannan kwanaki zai sa a dace da wannan lokaci.

2. Karatun Al-Qur’ani

Karanta littafi mai tsarki yana cikin abin da ake so a wannan kwanaki. A cikin wannan watan ne kuma dama dai aka saukar da Al-Kur’ani. Mutum zai samu babban rabo wajen karatun Kur’ani a kwanakin nan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sha ruwa da Gwamnonin Najeriya

3. Zikiri a koyaushe

Ambaton Allah abu ne mai lada kwarai da gaske kuma yawaita shi zai kai mutum ga babban rabo musamman a karshen wannan wata da ake ciki mai tarin falala da albarka inji Malamai.

4. Sadaka

A wannan lokaci kuma za a so mutum ya zama mai bada sadaka domin samun lada. Zai yi kyau idan da hali mutum ya dauki nauyin ciyar da marasa hali ko da da dabino ne a wannan lokaci.

5. I’itikafi

Abu ne mai kyau mutum ya shiga masallaci ya kebe kan sa da ibada musamman a ragowar wannan kwanaki na Ramadan. Mai I’itikafi ya kan rabu ne da harkokin Duniya ya bazama neman lahira watan Ramadan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel