Abba Gida Gida Ya Naɗa Sababbin Mukamai, Tsohon Mai Adawa da Gwamnati Ya Rabauta

Abba Gida Gida Ya Naɗa Sababbin Mukamai, Tsohon Mai Adawa da Gwamnati Ya Rabauta

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da jerin sababbin naɗe-naɗe da ƙara wa wasu manyan ma'aikata girma a gwamnatinsa
  • Sauye-sauyen sun haɗa da shigo da ƙwararru da matasa masu ƙwazo don tabbatar da inganci wajen tafiyar da mulkin jihar Kano
  • Daga cikin waɗanda suka samu muƙaman, akwai Auwal Lawan Aramposu a matsayin Mataimakin darekta janar a KAROTA

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - A wani mataki na ƙarfafa shugabanci da inganta ayyukan gwamnati, gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da jerin sababbin naɗe-naɗe a gwamnatin Kano.

Wadannan sauye-sauyen sun haɗa da shigo da ƙwararru da matasa masu ƙwazo, domin ƙarfafa aniyar gwamnatinsa ta samar da ingantaccen shugabanci da samun ci gaba.

Gwamnati
Gwamnatin Abba ta nada sababbin mukamai Hoto: Sunusi Bature D-Tofa/Auwalu Lawal Shaaibu
Asali: Facebook

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da darakta janar kan yaɗa labaran gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Fubara na iya dawowa: Tinubu na fusƙantar barazana kan dokar ta baci a majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mai adawa da Abba ya samu mukami

Sanarwar ta bayyana cewa an naɗa Auwal Lawan Aranposu a matsayin Mataimakin darekta janar na hukumar KAROTA da ke kula da zirga zirgar ababen hawa a jihar.

Aranposu, shi ne tsohon shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a karkashin mulkin APC, kuma ya taɓa zama mai na da shawara na musamman ga tsohuwar gwamnatin jihar.

Ya na daga cikin manyan masu sukar NNPP da gwamnatin Abba Kabir Yusuf a baya.

Amma tsohon 'dan Kwankwasiyyar ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki bayan ya fusata APC da ake shari'ar zaben gwamna.

Sauran wadanda Abba ya nada mukamai

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Hauwa Hassan Tudun Wada a matsayin Manajan darekta na hukumar kula da tsare-tsaren birane da rsaya Kano (KNUPDA).

Haka kuma ya naɗa Mustapha Muhammad a matsayin Sakataren yaɗa labarai na gwamna kuma mataimakin kakakin hukuma.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sabuwar barazana ta tunkaro Sanata Natasha kan zamanta a majalisa

Shi gogaggen ɗan jarida ne da ke da ƙwarewa fiye da shekaru ashirin, inda ya taɓa aiki a matsayin babban mai gabatar da shirye-shirye.

Gwamna Abba ya nada mai ba shi shawara

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Dr. Tukur Dayyabu Minjibir a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin noma.

Gwamna
Gwamna Abba ya naɗa masu kula da hukumomi a Kano Hoto: Sunusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Shi ne tsohon Manajan darekta na kamfanin samar da kayayyakin noma na Kano, kuma malami ne a jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya.

Baya ga waɗannan manyan nade-nade, gwamnan ya amince da haɓaka wasu manyan jami’an gwamnati guda biyu,

Wadanda gwamna Abba ya karawa girma

Gwamnatin Kano ta nada tsohuwar mai ba gwamna shawara kan harkokin labarai a mataki na daya, Zulaihat Yusuf Aji a matsayin Mataimakiyar manajan darekta ta rediyo Kano.

Sai kuma Injiniya Abduljabbar Nanono da ya samu karin girma zuwa Mataimakin manajan darekta na KHEDCO.

Sanarwar Sanusi Bature Dawakin Tofa ta kara da cewa dukkanin wadanda aka nada za su fara aiki nan take, tare da fatan za su taimaka wajen habaka ayyukan gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnatin Tinubu ta fadi gatan da za ta yi wa 'shugaban rikon kwarya'

Gwamna Abba ya ba sarakuna umarni

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarni ga dukkannin masarautun jihar guda hudu da su shirya gudanar da hawan karamar Sallah.

Umarnin na zuwa ne bayan an 'dan samu tsaikon gudanar da hawan cikin walwala tun bayan da aka fara dambarwar masarauta, lamarin da ‘yan sanda ke dangantawa da rashin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng