An Yi Amfani da Sunan Matar Gwamnan Katsina, An Damfari Mutane Naira Miliyan 197

An Yi Amfani da Sunan Matar Gwamnan Katsina, An Damfari Mutane Naira Miliyan 197

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu ma’aurata da wasu mutum biyu a kotun Kaduna bisa zargin damfara, satar kudi da wanke kudin haram
  • Ana zargin su da yaudarar mutane ta hanyar sojan gona da matar gwamnan Katsina, Fatima Dikko Radda, inda suka karbi miliyoyin Naira
  • Kotun ta bada umarnin a tsare su a gidan gyaran hali bayan sun musanta laifinsu, tare da dage sauraron bukatar belinsu zuwa 17 ga Maris, 2025

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu ma’aurata, Baba Sule Abubakar Sadiq da Hafsat Kabir Lawal, a gaban Mai shari’a Amina Bello ta babbar kotun jihar Kaduna.

Ana tuhumar su tare da wasu mutum biyu, Abdullahi Bala da Ladani Akindele, bisa zargin damfara, wanke kudin haram da satar kudi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi tabargazar sace sarki da dare, an kama mutum 5

EFCC ta yi magana da ta gurfanar da ma'aurata kan damfarar Naira miliyan 197
Kotu ta garkame ma'auratan da suka yi basaja da matar gwamnan Katsina suka yi damfara. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

An kama ma'aurata masu basaja da matar gwamna

A cikin wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta ce wadanda ake zargi sun karbi N197,750,000 ta hanyoyin yaudara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa an gurfanar da mutanen hudu a ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025, bisa tuhume-tuhume shida.

Musamman, ana zargin su da hadin baki don yaudarar mutane ta hanyoyi daban-daban, ciki har da yin sojan gona da uwar gidan gwamnan Katsina, Fatima Dikko Radda.

Jami’an tsaron farin kaya (DSS) ne suka fara kama su, amma daga bisa aka mika su ga EFCC saboda an gano laifin na da alaka da zambar kudi.

Yadda ma'auratan suka damfari mutane N197m

Daya daga cikin tuhume-tuhumen kamar yadda sanarwar ta nuna ya ce:

"Ku Baba Sule Abubakar Sadiq, Hafsat Kabir Lawal, Abdullahi Bala, da Ladani Akindele Ayodele, a watan Disamba 2024, a Kaduna, kun karɓi N89,000,000 daga Aminu Usman ta hanyar zamba.

Kara karanta wannan

Jami’in hukumar NIS ya tsunduma a matsala, an kama shi ya damfari gwamnati N17.6m

"Kun sa an tura maku kudin zuwa asusun banki na Taj Bank mai lamba 0009914725 mallakin Abdullahi Bala, bisa ikirarin cewa kuna da $53,300 da za ku sayar zuwa Naira, alhali kun san hakan ba gaskiya ba.
"Wannan laifi ne da ya saba wa sashe na 1(1) na Dokar Yaki da Damfara ta 2006, wanda ake hukunta shi a karkashin Sashe na 1(3) na dokar."

Bayan karanta tuhume-tuhumen, dukkanin wadanda aka gurfanar, sun musanta aikata laifuffukan da ake zarginsu da su.

Kotu ta iza keyar ma'auratan zuwa gidan yari

Lauyan EFCC, Bright C. Ogbonna, ya bukaci kotu ta saka ranar shari’a tare da bayar da umarnin a tsare wadanda ake tuhuma a gidan gyaran hali.

Lauyoyin kare wadanda ake tuhuma, M.S Katu (SAN), Jazuli Mustapha, da Paul A. Okachi, sun ce sun shigar da bukatar beli kuma sun shirya su ci gaba da shari’ar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka

Sai dai EFCC ta ki amincewa da bukatar belin, tana mai cewa tun da kotu ba ta shirya sauraron karar ba, to bai kamata a bayar da su beli ba.

Bayan sauraron hujjoji daga bangarorin biyu, Mai shari’a Amina Bello ta amince da bukatar masu gabatar da kara, inda ta bada umarnin a tsare wadanda ake zargi a gidan gyaran hali.

Mai shari’a Amina Bello ta dage sauraron bukatar belinsu zuwa 17 ga watan Maris, 2025.

Yadda miji ya taimakawa matarsa a damfara

Yadda Hafsat Kabir da mijinta ke damfarar mutane da sunan uwar gidan gwamnan Katsina
Hafsat Kabir Lawal, matar da ta hada kai da mijinta suna damfarar mutane da sunan Fatima Dikko Radda. Hoto:@officialEFCC
Asali: Twitter

Binciken EFCC ya nuna cewa Hafsat ta yaudari wadanda suka shigar da kara ne ta hanyar gabatar da kanta a matsayin daya daga cikin matan Gwamna Dikko Radda.

Ta hanyar wannan makirci, ta karbi N89,000,000 daga wani mutum, sannan ta karɓi N108,000,000 daga wani mutum na daban, kan cewa tana da $118,300 da za ta sayar masa.

Har ila yau, bincike ya nuna cewa mijinta, Baba Sadiq, shi ne ya ba ta layukan waya biyu da aka yi wa rijista da sunan Fatima Dikko Radda a manhajar Truecaller.

Kara karanta wannan

Bayan hallaka jama'a da karbe kudin fansa, mugun 'dan ta'adda ya gamu da karshensa

Bayan haka, ya nemi Ladani Akindele, wanda suka taba aiki tare a wani banki, da ya samo masa lambar wayar shugaban Unity Bank, Hafiz Bashir.

Ta hanyar hakan, Hafsat ta samu lambar Aminu Usman, wanda dan canji ne, sannan ta yaudare shi har ya ba ta N197,750,000.

An ce an tura kudin zuwa asusun banki na Abdullahi Bala, wanda shi ne na uku a cikin wadanda ake tuhuma, kuma daga nan aka raba kudin tsakanin su.

EFCC ta ce an bi hanyoyi daban-daban don wanke kudin da aka samu ta hanyar damfara.

EFCC ta gurfanar da ma'aurata kan zambar N410m

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar EFCC na zargin wasu ma’aurata a Kano, Aisha Malkohi da Abubakar Mahmoud, da badakalar kudi mai yawa.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa, na tuhumar ma'auratan da damfarar Naira miliyan 410, inda jami'an EFCC suka samu nasarar cafke matar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel