Jigawa: Amarya Ta Watsawa Kishiyarta Tafasasshen Ruwan Zafi, Ta Zama Silar Ajalinta

Jigawa: Amarya Ta Watsawa Kishiyarta Tafasasshen Ruwan Zafi, Ta Zama Silar Ajalinta

  • Rundunar ‘yan sandan Jigawa ta kama Rukayyah Amadu, da ake zargin ta kashe kishiyarta ta hanyar watsa mata tafasasshen ruwan zafi
  • A wani mummunan hari, an tsinci gawar wata amarya, Zainab Ibrahim, a Warware Quarters, Hadejia, inda aka yi mata yankan rago.
  • A garin Gwaram, an gano gawar wani almajiri, Bashir Adamu, an yanke masa kai, shi kuma ana zargin an kashe shi don safarar sassan jikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wata mata mai shekaru 20, Rukayyah Amadu, bisa zargin kashe kishiyarta, Asiyah Amadu, mai shekaru 30.

Rahoton rundunar na farko ya nuna cewa Rukayyah Amadu ta watsawa kishiryata Asiya Amadu tafasasshen ruwan zafi, wanda ya zama ajalinta.

Rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata da ta kashe kishiyarta da tafasasshen ruwan zafi
Ana zargin wata amarya ta kashe kishiyarta da tafasasshen ruwan zafi a jihar Jigawa. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse ranar Alhamis, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amarya ta kashe kishiyarta da ruwan zafi a Jigawa

A cewar SP Shi’isu, lamarin ya faru ne a ranar 24 ga Fabrairu, 2025, a kauyen Buju da ke karamar hukumar Dutse, bayan wata takaddama da ta barke tsakanin matan biyu.

Sanarwar mai magana da yawun 'yan sandan ta ce:

“Asiyah Amadu ta samu munanan raunuka sakamakon konewa da ta yi bayan an watsa mata ruwan zafi, inda aka garzaya da ita babban asibitin Dutse don ceto ranta.
"Amma, abin takaici, likitoci sun tabbatar da mutuwarta a ranar 4 ga Maris, 2025, da misalin karfe 9:00 na safe."

‘Yan sanda sun ce sun kama Rukayyah Amadu kuma sun mika ta ga sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da gudanar da bincike.

“Yayin bincike, Rukayyah ta amsa laifinta. A halin yanzu, ana ci gaba da bincike domin gano cikakken yanayin da lamarin ya faru,” inji SP Adam.

Jigawa: An kashe wata amarya a garin Hadejia

Kara karanta wannan

An gano shugaban kasar da ya kafa kungiyar Lakurawa da yadda suka shigo Najeriya

A wani lamari makamancin wannan, an tsinci gawar wata amarya mai suna Zainab Ibrahim, kwance cikin jini a gidanta da ke rukunin gidaje na Warware, karamar hukumar Hadejia.

Kakakin 'yan sandan Jigawa, SP Adam ya ce:

“Jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO na Hadejia sun isa wurin da abin ya faru, inda suka gano cewa an yiwa amaryar yankan rago."

Sanarwar ta ce ‘yan sanda sun garzaya da ita zuwa babban asibitin Hadejia, inda a nan ne likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Mai magana da yawun 'yan sandan, SP Adam ya ce an fara bincike domin gano wanda ko wadanda suke da hannu a aikata wannan mummunan kisan.

An kashe wani karamin yaro a Gwaram

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan ayyukan ta'addanci da ke faruwa a jihar Jigawa
Jigawa: 'Yan sanda sun fitar da rahotanni kan kisan wata budurwa da wani almajiri. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A wani harin ta’addanci, an gano gawar wani yaro mai shekaru 14, Bashir Adamu, a kusa da kauyen Jikas-Dabaja da ke karamar hukumar Gwaram.

An tsinci gawar Bashir, wanda ake kyautata zaton cewa almajiri ne, ba tare da kai ba, kuma an yi masa munanan raunuka a sassan jikinsa.

Kara karanta wannan

"Jonathan ya yi bankwana da siyasa," PDP ta magantu kan fito da shi takara

Iyalan yaron sun tabbatar da cewa ya bace na tsawon kwanaki biyu kafin a gano gawarsa.

“Binciken farko ya nuna cewa ana zargin an kashe shi ne saboda safarar sassan jikin dan Adam,” in ji SP Adam.

Rundunar ‘yan sandan Jigawa ta tabbatar da cewa za ta gudanar da bincike mai zurfi domin kamo wadanda suka aikata wadannan laifuffuka.

Ta bukaci jama’a da su bayar da hadin kai don taimakawa jami’an tsaro wajen dakile irin wadannan manyan laifuka.

Mata ta kashe kishiryata mai juna biyu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami'an tsaro sun gurfanar da wata mata mai suna Fatima Abdul Rahman, a gaban kotu bisa zargin kashe kishiyarta, Adizat Abdul Rahman.

Ana zargin Fatima ta caccaka wa Adizat wuka a wuya, wanda hakan ya zama ajalinta, yanzu ana tuhumarta da laifin kisan kai, wanda doka ta tanadi hukunci mai tsauri a kansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng