Zafin Kishi: Wata Mata Ta Kashe Kishiyarta Da Ke Ɗauke da Juna Biyu a Legas

Zafin Kishi: Wata Mata Ta Kashe Kishiyarta Da Ke Ɗauke da Juna Biyu a Legas

  • An gurfanar da Fatima a gaban kotu bisa laifin kashe kishiyar ta mai ɗauke da juna biyu
  • Fatima ta gano mijin ta ya ƙara aure, inda zafin kishi ya rinjaye ta ta aikata ɗanyen aiki
  • Fatima ta yi amfani ne da wuka wajen kashe kishiyar ta ta Adizat

Legas - Jami'an tsaro a yankin Ikoyi sun gurfanar da wata mata mai suna Fatima Abdul Rahman 'yar kimanin shekaru 42 a gaban kotu bisa tuhumar ta da kashe Kishiyar ta mai suna Adizat Abdul Rahman ta hanyar caccaka ma ta wuƙa a wuyan ta.

An dai gurfanar da Fatima ne a ranar Talata a gaban Mai shari'a P. E Nwaka a Kotun Majistire da ke zamanta a Yaba bisa tuhumar ta da laifin kisan kai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗi Matsalar da Aka Samu Da halin da Ragowar 'Yan Najeriya Ke Ciki a Sudan

Kotun majistire
Wata Mata Ta Kashe Kishiyarta Da Ke Ɗauke da Juna Biyu a Legas Hoto: Punch ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zafin kishi ne ya sanya matar kashe amaryar minjin ta

Wannan mummunan lamarin dai ya faru ne a unguwar Ilejo da ke a yankin Ikorodu na jihar Legas inda mata mai suna Fatima Abdul Rahman taje har gida ta kashe amaryar mijin ta wacce take ɗauke da juna biyu a lokacin faruwar lamarin.

Jaridar Punch ta wallafa cewa zafin kishin cewa mijin ta ya ƙara aure ne ya sa Fatima wacce 'yar Asalin ƙasar Chadi ce aikata wannan ɗanyen aiki a yayin da ta samu labarin cewa ya ƙara auren.

Ta yi ɓadda kama ne inda ta je gidan a matsayin cewa ita malamar asibiti ta jinya ce inda daga nan ne ta samu damar caccaka ma Adizat wuƙar da ta yi sanadin ajalin ta.

Kara karanta wannan

"Na Gaji": Wata Yar Najeriya Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurensu, Sannan Ta Damƙa Mata Motocci Da Gidajen Mijinta

Wani maƙocin gidan da abun ya faru ne ya ga matar a lokacin da ta shiga gidan

Wani maƙocin gidan mamaciyar ne ya gan ta a yayin da ta ke shiga gidan, inda daga bisani kuma aka tarar da gawar matar wacce aka yiwa munanan raunuka ta hanyar caka ma ta wuƙa a wuya.

Jami'i mai shigar da ƙara Thomas Nurudeen ya ce matar da ake tuhuma ta aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Afrilu 2023, da misalin 12:40 na rana a unguwar Ilejo kan titin Ijede da ke a yankin Ikorodu na jihar Legas.

Kotu ta ɗage sauraron shari'ar zuwa 25 ga watan Mayun da muke ciki sannan ta kuma bada umarnin a ci gaba da tsare matar da ake tuhuma har zuwa lokacin.

Batun kashe-kashe dai tsakanin mata wani abu ne da ya zama ruwan dare, inda ko a kwanakin baya sai da jaridar Thisday ta wallafa labarin wata mata 'yar kimanin shekaru 50 da ta kashe kishiyar ta a Bauchi.

Kara karanta wannan

"Na Wanke Shi Tas", Dirarriyar Budurwa Ta Yaudari Mahaifinta a Matsayin Budurwarsa, Ya Tura Mata Kudade

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu a Zaria

A wani labarin na daban kuma, 'yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da wasu mutane su huɗu a yayin da suka kai wani farmaki a garin Zaria da ke jihar Kaduna.

Lamarin dai ya faru ne a daren ranar Litinin inda aka ce 'yan bindigar waɗanda suka zo da yawa sun kawo farmakin ne da misalin ƙarfe 09:40 na dare inda suka je gidan wani jami'in hukumar kwastam dake a yankin Kofar Kona cikin Zaria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel