Dangote Zai Iya Shiga Matsala: Za a Kafa Sababbin Matatun Man Fetur 3 a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta amince da gina sababbin matatun mai uku da za su kara yawan man da ake tacewa zuwa ganga 140,000 a kowace rana
- Hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA ta bayyana cewa samun karin matatun zai tabbatar da wadatuwar man fetur a fadin kasar nan
- NMDPRA ta bai wa kamfanonin Eghudu, MB Refinery da HIS Refining lasisin gina matatun mai a jihohin Edo, Delta da Abia don karfafa tace mai
- A zantawarmu da Alhaji Abubakar Katsina, ya ce akwai sa ran nan da shekara biyar masu zuwa farashin mai ya sauka zuwa yanda talaka zai iya saya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da gina sababbin matatun mai uku a karkashin hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA.
A sanarwa da NMDPRA ta wallafa a shafukanta a ranar Juma’a, an bayyana cewa wadannan matatun za su kara tace ganga 140,000 a kowace rana a Najeriya.

Source: Getty Images
Gwamnati ta amince a gina matatun mai 3
A shafinta na X, NMDPRA ta ce an bai wa kamfanin Eghudu da ke Edo lasisin gina matatar mai mai karfin tace ganga 100,000, yayin da kamfanin MB Refinery a Delta zai gina matata mai tace ganga 30,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, HIS Refining and Petrochemical Ltd da ke Abia ya samu lasisin gina matatar mai mai karfin tace ganga 10,000 a kowace rana.
Shugaban NMDPRA, Engr. Farouk Ahmed, ne ya mika wadannan lasisin ga shugabannin kamfanonin da suka samu damar gina matatun.
Matatun da aka amince a gina a farkon 2025
A farkon shekarar nan, NMDPRA ta bai wa kamfanin MRO Energy Ltd lasisin gina matatar mai mai karfin tace ganga 10,000 a garin Imode da ke Ughelli, jihar Delta.
Haka nan, a watanni biyu da suka gabata, an bai wa kamfanin Process Design and Development Ltd damar gina matatar da za ta rika tace ganga 27,000 a Gombe.
Wannan ci gaban yana nuni da cewa Najeriya na da kimanin matatun mai guda 14 da ke aiki a halin yanzu, masu girma, da aka gina su a tsari na zamani.

Source: Twitter
'Yan kasuwa na zargin gwamnati da ba da fifiko
A farkon shekarar nan, kungiyar masu gidajen mai ta PETROAN ta sanar da hadin gwiwa don kafa sabuwar matatar mai karfin tace ganga 50,000 a kullum.
Duk da karuwar yawan matatun mai, mafi yawan su ba sa aiki da cikakken karfinsu, ko kuma sun daina aiki gaba daya.
Wani babban kalubale shi ne rabon danyen mai ga matatun gida. Manyan ‘yan kasuwa sun koka kan rashin wadataccen mai daga gwamnati.
Sun zargi hukumomi da fifita shigo da man fetur daga kasashen waje maimakon rabawa matatun cikin gida isasshen danyen mai da za su tace.
"Muna fatan farashin fetur ya sauka" - Abubakar
A zantawarmu da wani dan kasuwar mai a Katsina, Alhaji Abubakar Katsina, ya ce akwai sa ran nan da shekara biyar masu zuwa farashin mai ya sauka zuwa yanda talaka zai iya saya.
Alhaji Abubakar ya ce:
"Yanzu an samu 'yan kasuwar da ke kara fahimtar fa'idar bude matatun mai, don haka, nan gaba za a samu matatu masu yawa da ke tace mai a kasar nan.
"Idan hakan ta tabbata, to dole farashin ya rika sauka, saboda za a samu gasa a tsakaninsu, babu matatar da za ta so manta ya rika yin kwantai saboda tsadar ta yi."
Amma da aka tambaye shi game da daidaita farashin man, Alhaji Abubakar ya ce:
"Idan ka duba matatar Dangote, za ka ga tana rage farashin ne gwargwadon farashin duniya. To haka su ma sauran matatu za su rika yi.
"To amma wannan tsarin ya fi a kan ace wani kamfani ko hukuma ce za ta rika kayyade farashin man, wanda ke kawo sabanin farashi da rashin daidaituwarsa."
Shirin Dangote na gaba bayan gina matatar mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shahararren attajirin Najeriya da Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana abin da ya fi mai da hankali akai a halin yanzu.
Dangote ya ce yana hutawa bayan kammala gina matatar mai tasa, wacce ta lashe sama da dala biliyan 20. Dangote ya gina matatar man a Lekki, jihar Legas, wacce tuni ta fara aiki.
Asali: Legit.ng


