Tada Farashi: NMDPRA ta Garkame Gidajen Mai 14 a Jihar Kano

Tada Farashi: NMDPRA ta Garkame Gidajen Mai 14 a Jihar Kano

  • Hukumar kula da farashin man fetur na jihar Kano ta garkame gidajen mai 16 bayan kamasu da laifin siyar da mai sama da daidaitaccen farashi
  • Hakan yazo ne bayan kama gidajen mai suna siyar da mai kan N290, N295 da N300 duk lita daya, yayin da gidajen man gwamnati ke siyarwa kan farashin N185
  • Shugaban hukumar ya ce, akwai tsauraran matakai da horo da aka tanadarwa wanda ya siyar da mai sama da farashin da aka daidaita, irinsu kwace lasisi, ko biyan N150,000 ga duk wurin bada mai daya

Kano - Hukumar kula da farashin man fetur ta Najeriya ta garkame a kalla gidajen 14 , NMDPRA reshen jihar Kano ta dauki matakin ne saboda yadda suke siyarwa kwastomomi kayayyakinsu sama da farashin da aka ka'idance, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kebbi: Jirgin Ruwa ya Nitse da Sama da Mutum 100, Manoma 10 Sun ce ga Garin ku

Man Fetur
Tada Farashi: NMDPRA ta Garkame Gidajen Mai 14 a Jihar Kano. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Hukumar kula da farashin man fetur da jihar Kanon ta garkame gidajen mai masu zaman kansu ne, saboda yadda suke sai da man fetur kan N290, N295 da N300 duk lita daya.

Yayin zantawa da manema labarai game da hukuncin, shugaban NMDPRA na Kano, Aliyu Muhammad Sama ya ce, duk da ba a saran 'yan kasuwa su saida mai kan farashi mai sauki kamar na manyan 'yan kasuwa, amma bai kamata su sanya farashi dai tsauri haka ba.

TheCable ta rahoto, a cewarsu gidajen mayukan sun janyo hukuncin kwace lasisinsu ko kuma cinsu tarar N150,000 ga duk wajen bada mai daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ya bayyana,:

"Idan ka duba, gidajen man gwamnati na saidawa kan farashi mai sauki na N185 duk lita daya. Mun san ba abu bane mai yuwuwa a ce 'yan kasuwa su siyar kan wannan farashin, duba da yadda suke ikirarin suna siya kan farashi mai tsada.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

"Amma a yau a jihar Legas masu saida mai suna siyarwa kan N230 duk lita daya ga 'yan kasuwa, saboda haka da wannan farashin mun san cewa ba zasu sa farashin kasa da kudin da suka siya ba. Amma ba za ka siyar kan N300, ko N290 duk lita ba saboda gwamnati na biyan N45 duk lita kamar yadda matata ta bayyana.
"Idan ta aka tsaida farashi tsakanin N230 zuwa N280, ka cire N45 daga tsadajjen farashin, za ka samu N235, a kalla zamu sa ran ribar N15.
“Saboda haka, 'yan kasuwa zasu iya siyarwa kasa da N290 kuma su samu riba bai kyau. Duk da a matsayinmu na hukuma, bama da alhakin tsaida farashi amma bazamu laminci farashi mai tsada wanda al'umma basu amince dashi ba.”

- A cewarsa.

Haka zalika, shugaban hukumar ta jihar ya kara da cewa, hukumar daidaita farashin ta dakatar da kasuwancin 'yan kasuwa 16 don ta horar dasu kan abun da suka aikata.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Hayaki Ya Turnuke Wasu Ma’aurata Har Lahira a Kano

"Ga kowanne gidan man da yaki saidawa kan farashin da aka daidaita, mun dakatar da kasuwancinsu, yayin da a halin yanzu mun tsaida kasuwancin gidajen mai 16 wanda hakan na nufin sun rasa damar siyan mai da kudin daidaito.
"Muna da doka mai tsanani ta daidaita farashi, wanda ya kunshi kwace lasisi, biyan tarar N150,000 ga duk wurin bada mai daya da kuma gurfanar da masu laifi.”

- Kamar yadda Sama ya bayyana.

Gidajen man da aka garkame sun hada da; gidan man Azman, wurin titin Maiduguri , Red star na titin Zaria , AY Maikifi yammacin Bypass, SID titin Zaria, da gidan man Audu Manager kan titin Maiduguri.

Sauka sun hada da Rumi Holdings, titin Maiduguri, Rabash enterprises Nigeria Limited, IDM Makole Nigeria Limited, Alhaji Ahmadu Ila and Sons Ltd, titin Maiduguri, Haab investment Limited kan titin Hotoro yammacin bypass.

Asali: Legit.ng

Online view pixel