BUA zai kafa matatar danyen mai da kamfanin sinadarai a Jihar Akwa Ibom

BUA zai kafa matatar danyen mai da kamfanin sinadarai a Jihar Akwa Ibom

Kamfanin BUA Group, daya daga cikin manyan masu harkar kayan abinci da sarrafa ma’adanai a Afrika, zai gina matatar danyen mai a Najeriya.

BUA Group ya shiga wata yarjejeniya da kamfanin Axens na kasar Faransa, wanda zai taimaka masa wajen gina katafaren matatar mai a jihar Akwa Ibom.

Jaridar Premium Times ta ce wannan matata da za a gina za ta rika tace ton miliyan 10 na danyen mai a shekara, sannan kuma za ta rika samar da sinadarai.

Bayan ganga 200, 000 na mai da za a rika tacewa a kullu-yaumin, sabon kamfanin zai rika samar da sinadaran Euro-V fuels da Polypropylene a Najeriya.

Shugaban BUA, Abdul Samad Rabiu da kuma takwarsansa na Axens, Jean Sentenac, su ka rattaba hannu a wannan yarjejeniya a gaban Mista Franck Riester.

Franck Riester shi ne ya wakilci ministan kasuwancin kasar waje da jawo masu hannun jari na Faransa.

KU KARANTA: An gama aikin kamfanin takin zamanin Dangote - Sabo Nanono

BUA zai kafa matatar danyen mai da kamfanin sinadarai a Jihar Akwa Ibom
Axens zai ginawa BUA matata a Akwa Ibom
Source: Twitter

Kamar yadda BUA ya bayyana, ya zabi ya hada-kai da kamfanin Axens a wannan aiki ne saboda irin kaurin-sunan da ya yi wajen kwarewa da kuma kayan fasaha.

Da zarar an kammala wannan kamfani, za a rika fitar da man gasoline, man jirgin sama, da bakin mai wanda za a rika amfani da shi a Najeriya da kasashen kewaye.

Bugu da kari, Najeriya za ta samu sindarin propylene wanda ake amfani da shi wajen yin robobi. Hakan zai sa Najeriya ta rage dogara da shigo da kaya daga ketare.

“A jinin BUA ne kirkirar kasuwanci mai kyau da zai daure. Ka duba kamfanin simintinmu, ya na cikin wanda su ka fi kowane tsayuwa, haka sukarinmu." Inji Rabiu.

Najeriya mai arzikin mai ta dogara da matatun kasashen waje ne domin tace man ta. Yanzu haka irinsu Aliko Dangote su na shirin kammala gina matatar mai a Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel