Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Ya Rasu Yana da Shekaru 72
- Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Dr. Doyin Okupe, likita kuma tsohon hadimin shugabannin kasa, yana da shekara 72 a duniya
- Marigayin ya shafe shekaru 16 yana fama da ciwon daji, inda aka yi kokarin yi masa magani a kasar Isra’ila, amma ba a dace ba
- Okupe ya taba zama kakakin jam'iyyar NRC, hadimin Obasanjo da Jonathan, sannan daga baya ya jagoranci yakin neman zaben LP a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun - Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da ce Dr. Doyin Okupe, likita kuma tsohon hadimin shugabannin Najeriya, ya rasu yana da shekara 72.
Majiyoyi daga iyalin Dr. Doyin Okupe sun tabbatar da cewa marigayin ya dade yana fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa.

Asali: Facebook
Tsohon hadimin shugaban kasa ya rasu
SaharaReporters ta rahoto cewa cewa marigayi Okupe ya sha fama da cutar daji, wacce ta yanke masa hanzari a karshen rayuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Oktoba 2023, rahotanni suka bayyana cewa an kwantar da Okupe a asibiti sakamakon kamuwa da ciwon daji a mafitsara.
Daga bisani, aka samu rahoton cewa an tafi da shi zuwa kasar Isra'ila don neman magani, amma jikin nashi ya ci gaba da tabarbarewa.
An rahoto cewa an fara gano ciwon daji a jikin Okupe shekaru 16 da suka wuce, daga baya kuma ya kamu da cutar 'sarcoma' a kafadarsa.
Mutuwar Dr. Doyin Okupe a ranar Juma'a, 7 ga watan Maris din 2025 kamar yadda The Nation ta ruwaito, ta kawo karshen wannan doguwar jinya da ya yi fama da ita.
Rasuwarsa bar babban gibi a harkar siyasa da fannin yada labarai a Najeriya yayin da ake jiran bayanin lokacin jana'izarsa daga iyalansa.
Tarihin rayuwa da na shigarsa siyasa
Legit Hausa ta fahimci cewa Okupe ya fito ne daga garin Iperu, da ke jihar Ogun, inda mahaifinsa, Chief Matthew Adekoya Okupe, ya yi aikin banki.
Rahoto daga shafin WikiPedia ya nuna cewa Okupe ya yi karatu a makarantar St. Jude's da kwalejin College a Legas kafin ya wuce jami’ar Ibadan, inda ya yi karatun likitanci.
A matsayinsa na likita, ya kafa cibiyar kiwon lafiya ta Royal Cross a Obalende, jihar Legas, tare da wasu abokansa likitoci.
A lokacin jamhuriya ta uku, Okupe ya zama mai magana da yawun jam’iyyar NRC a matakin kasa.
Takara da matsayin da ya rike a jam'iyyar LP

Asali: Twitter
Bayan haka, an rahtoo cewa ya zama mai taimaka wa Shugaba Olusegun Obasanjo kan harkokin yada labarai.
A karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan, an nadashi a matsayin babban mai ba da shawara kan harkokin jama’a.
A shekarar 2022, ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar LP kafin daga baya ya janye daga takarar.
An nada Okupe a matsayin darakta janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023.
A watan Janairun shekarar 2024, Legit Hausa ta rahoto cewa Okupe ya fice daga jam’iyyar saboda sabanin akida da ra’ayoyin siyasa.
Doyin OKupe ya yi murabus daga daraktan LP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Doyin Okupe ya sauka daga mukaminsa na Darakta Janar na tawagar yakin neman zaben shugabancin kasa na Peter Obi da Datti Baba-Ahmed.
Ya bayyana murabus dinsa ne cikin wata wasika da ya aikewa Peter Obi, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyya LP, mai dauke da kwanan wata 20 ga Disamba, 2022.
Asali: Legit.ng