Muhimman Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani game da Sabon Tsarin Cire Kuɗi a ATM

Muhimman Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani game da Sabon Tsarin Cire Kuɗi a ATM

Bankunan kasuwanci a Najeriya sun fara aiwatar da sabon tsarin da babban bankin Najeriya watau CBN ya ɓullo da shi ga duk wanda ya yi amfani da na'urar ATM.

Bankunan sun fara ɗaukar N100 ga kowane abokin mu'amala da ya cire N20,000 daga na'urar cire kuɗi watau ATM da ke cikin harabar banki.

Na'urar ATM.
An fara aiwatar da sabon tsarin cire kudi da ATM Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton Tribune ya nuna cewa bankuna sun kuma fara zaftare N600 daga asusun duk wanda ya cire N20,000 a ATM da ke wajen bankuna.

Wannan sabon tsari dai bankin CBN ne ya ɓullo da shi kuma ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 10 ga Fabrairu, 2025.

Babban bankin ya umarci bankunan kasuwanci su fara aiwatar da tsarin daga ranar 1 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan shafin, Legit Hausa ta tattaro maku muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon tsarin, ga su kamar haka:

Kara karanta wannan

Kwamishinonin El Rufa’i sun bayyana gaskiyarsu kan zargin karkatar da N1.37bn

1. Cire kudi daga ATM da ke cikin banki

Idan kwastoma ya cire N20,000 daga na'urar ATM da ke cikin harabar kowane irin bankin kasuwanci (on-site ATM), za a caje shi N100.

Kwastomomin da ke amfani da ATM na bankin da suka buɗe asusu a ciki ba za za caje su ko ƙwandala ba, kamar yadda tsarin yake a baya, rahoton Naira Metrics.

CBN ya ce kwastoma zai ga adadin kuɗin da za a ɗaukar masa a allon na'urar ATM ɗin kafin ya ƙarisa cire kuɗin.

2. Cire kudi daga ATM da ke waje

A Najeriya, wasu bankunan kasuwanci su kan sanya na'urar ATM a wurin da ba banki ba, kamar babbar makaranta, ko jami'a, gidan mai da sauransu.

Idan kwastoma ya cire kudi daga na'urar ATM da ke wajen harabar banki, kamar a manyan kantuna ko gidajen mai, za a ɗaukar masa N600.

Wannan kuɗi N600 da za a zaftare sun ƙunshi N100 na cire kuɗi da kuma ƙarin N500 na amfani da ATM da ke wajen harabar bankuna.

Kara karanta wannan

An fara cike fom domin samun tallafin noman Naira miliyan 1 na Sanata Barau

Tsarin CBN.
Sabon tsarin cire kudi a CBN ya fara aiki ranar 1 ga watan Maris, 2025 Hoto: @Centbank
Asali: Getty Images

3. Cire kudi a ATM na ƙasashen waje

Masu tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ketare kama daga ɗalibai da suka tafi karatu ko masu zuwa shaƙatawa ko aiki, duk wanda cire kudi ya kama shi a kasar waje zai iya amfani da ATM ɗinsa.

Ga waɗanda ke cire kudi a ATM na ƙasashen waje, za a caje su bisa ƙimar da ke kan kuɗin da suka cire, wato za su biya ainihin kuɗin aiki da mai ATM ya gindaya.

4. Dalilin da ya sa CBN ya bullo da tsarin

Bankin CBN ya ce ɗaukar wannan mataki game da amfani da ATM ya zama dole saboda hauhawar farashin kayan ayyukan banki da kuma ƙoƙarin inganta tsarin cire kuɗi.

Bugu da ƙari, CBN ya bayyana cewa matakin na da nufin inganta tsarin ATM, rage hauhawar farashi, da kuma ƙarfafa saka hannun jari a fannin harkokin banki.

CBN ya yi wannan bayani ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur ya kama hanyar ƙara araha, sauƙi zai lulluɓe ƴan Najeriya

Wannan sabuwar doka ta CBN ta kawo ƙarshen damar da ke bai wa kwastomomi damar cire kuɗi kyauta sau uku a wata daga ATM ba tare da an ɗauki ko sisi.

5. Ƙalubalen da CBN ya fara fuskanta

Ƙungiyoyin fararen hula da ɗaiɗaikun mutane sun yi fatali da wannan sabuwar doka, inda suka bayyana cewa ba abin da tsarin zai haifar face ƙarin wahala ga ƴan ƙasa.

Kungiyar SERAP mai gwagwarmayar kare haƙƙin tattalin arziki, ta maka CBN a kotu, tana mai cewa sabon tsarin ɗaukar kudin rashin adalci ne ga ƴan ƙasa.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafin X, SERAP ta buƙaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da CBN daga aiwatar da wanna tsarin.

Na'urar ATM.
Mutane sun nuna damuwa da wannan tsari na CBN Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

6. Ƙorafe-ƙorafen ƴan Najeriya

Sabon tsarin ya jawo ce-ce-ku-ce daga kwastomomin bankuna da al’umma, inda wasu ke ganin cewa zai ƙara matsi ga talakawa, musamman masu amfani da ATM a waje.

Kara karanta wannan

El Rufa'i: Kotu ta umarci ICPC ta kwato sama da N1bn da aka karkatar a Kaduna

Abdulhafiz Muhammad, wani mai amfani da First Bank ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan tsarin bai zo a lokacin da ya dace ba.

Matashin ya bayyana cewa ya kamata babban banki ya sake nazari, ya janye wanna dokar domin za ta karawa mutane wahala ne kawai.

Abdulhafiz ya ce:

"Ba mu da First Bank a Ɗanja, ina ga shekaran jiya ne na je Access na cire kuɗi, na ga sun cire wannan adadin da suka ambata.
"Ina ganin ƙaƙabawa mutane wanann tsarin bai kamata ba a yanzu da ake fama da wahala, kowa ta abinci yake yi, ya kamata gwamnati ta sake nazari kan lamarin."

CBN ya daƙile hauhawar farashin kaya

A wani labarin, kun ji cewa babban bankin ƙasa watau CBN ya ce ba don manufofin da ya ɓullo da su ba, da hauhawar farashi ya tsallake 40% kafin karewar 2024.

Babban bankin ya yi alkawarin ci gaba da bin tsare-tsarensa na kudi don shawo kan hauhawar farashin kaya a 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng