Mubarak Bala da Ƴan Arewa 4 da Aka Taɓa Yankewa Hukuncin Kisa kan Ɓatanci ga Annabi

Mubarak Bala da Ƴan Arewa 4 da Aka Taɓa Yankewa Hukuncin Kisa kan Ɓatanci ga Annabi

Kano - Batun ɓatanci ga addini na ci gaba da tayar da kura a Najeriya, ƙasa da ke da yawan al'ummomin da ke da ra'ayoyi mabanbanta kan addini.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Hukuncin da aka yankewa Mubarak Bala, Yahaya Sharif, da wasu mutane uku saboda ɓatanci ya sake janyo muhawara kan 'yancin yin addini, haƙƙin ɗan Adam, da kuma huldar da ke tsakanin addini da dokokin ƙasa.

Rahoton 'yan Arewa 5 da kotu ta yanke wa hukunci kan tuhume-tuhumen batanci
Kotu ta yankewa wasu 'yan Najeriya 5 hukunci kan kama su da laifuffukan batanci. Hoto: @MubarakBala, @AbdussamadAhma1
Asali: Twitter

Wannan rahoto zai binciko tushen waɗannan shari'o'i, tasirin su ga doka da al'umma, da tattaunawar da ke gudana kan dokokin ɓatanci a Najeriya.

Mubarak Bala: Matashin da ke sukar addini

Mubarak Bala, ɗan Najeriya da ya shahara a wajen sukar addini, ya shiga hannu a watan Afrilu na 2020 a Kaduna kan zargin batanci ga Musulunci a shafukansa na sada zumunta.

Kara karanta wannan

"Sai Atiku," Ana tunanin matsalolin Najeriya sun fi karfin gwamnatin Tinubu

An cafke shi ne bayan koke daga wasu kungiyoyin addini da suka ce sakonnin da yake wallafawa cin mutunci ne ga Annabi Muhammad (SAW).

Duk da ƙorafe-ƙorafe daga ƙasashen duniya da kira ga a sake shi, wata kotun jihar Kano ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 24 a watan Afrilu 2022 bayan da ya amsa laifinsa.

Shari'ar Mubarak Bala ta janyo damuwa game da yadda tsarin shari'a ke kula da masu akidar rashin addini a Najeriya.

Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun bayyana cewa hukuncin da aka yankewa Bala ya saba wa 'yancin faɗar albarkacin baki da kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa ke baiwa kowane mutum.

Mubarak Bala ya sami 'yanci

Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 25 a gidan yari bayan amsa laifin batanci
Mubarak Bala ya sami 'yanci bayan shafe shekaru sama da hudu yana tsare. Hoto: @MubarakBala
Asali: Twitter

Legit Hausa ta rahoto cewa an saki Mubarak Bala, shugaban kungiyar HAN, daga gidan yari a ranar a watan Janairun 2025, bayan shafe kusan shekaru huɗu da rabi a tsare.

Kara karanta wannan

Kotu ta dakile shirin Trump kan yan gudun hijira game da yancin zama ɗan kasa

A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na intanet, hukumar kare 'yancin addini ta Amurka (USCIRF) ta nuna jin daɗinta da wannan mataki.

Kwamishiniyar USCIRF, Vicky Hartzler ta shaida cewa:

“Mubarak Bala ya fuskanci babbar rashin adalci. Bai kamata wani mutum ya shafe shekaru 24 ko wani lokaci a gidan yari saboda wallafa wani bayani mara tashin hankali a sada zumunta ba."

Duk da cewa an sake shi, akwai fargabar cewa rayuwarsa na cikin haɗari, inda aka ce ya shiga buya saboda barazanar da yake fuskanta daga masu tsauraran ra’ayi da ke kallon akidarsa a matsayin abin ki.

Yahaya Sharif: Mawaki da ake zargi da batanci

An cafke Yahaya Sharif-Aminu, wani mawakin Kano mai shekaru 22, a watan Maris na 2020 bayan wata waƙa da ya wallafa a WhatsApp da aka ce ta ƙetare iyakar mutunta addinin Islama.

Majalisar Turai ta yi magana kan ci gaba da tsare mawaki Sharif-Aminu
An yankewa mawaki Sharif-Aminu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan batanci ga Annabi. Hoto: @Europarl_EN
Asali: Twitter

A cewar rahotanni, baitocin waƙarsa sun ɗaukaka wani mutum sama da Annabi Muhammad (SAW), wanda ya jawo fushin al'umma da zanga-zanga a yankinsa.

Kara karanta wannan

Da gaske Sarkin Musulumi ya sanya kayan bokaye? Hoto ya bayyana, an gano gaskiya

A sakamakon haka, kotun Shari’a ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, hukuncin da ya zama daya daga cikin mafi tsauri a tarihin Najeriya dangane da ɓatanci ga addini.

Bayan suka daga kungiyoyi kamar Amnesty International, mun rahoto cewa, awaki Sharif-Aminu ya ɗaukaka ƙara.

A watan Janairu 2021, Babbar Kotun jihar Kano ta soke hukuncin kisan amma ta bada umarnin sake shari’a, wanda ya jefa rayuwarsa cikin rashin tabbas har yanzu.

A watan Fabrairun 2025, Legit Hausa ta rahoto cewa majalisar Tarayyar Turai ta amince da wani kudiri da ke adawa da yada Najeriya ke tsarewa da yanke hukuncin kisa ga masu fuskantar tuhuma kan ɓatanci.

Majalisar ta bukaci a saki Sharif-Aminu nan take, tare da jaddada bukatar tabbatar da 'yancin faɗin albarkacin baki da 'yancin shari’a a Najeriya.

Sauran Mutane Uku da Aka Yanke wa Hukunci

Baya ga Bala da Sharif-Aminu, wasu mutum uku sun fuskanci hukunci saboda tuhume-tuhumen batancinci ga addini a jihohi daban-daban a Arewa.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Trump zai binciki zargin tallafawa Boko Haram daga Amurka

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Kotu ta yankewa Abduljabbar Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya
Kotu ta yankewa Abduljabbar hukuncin kisa bayan samunsa da laifin batanci ga Annabi. Hoto: Abduljabbar Kabara
Asali: UGC

A watan Yulin 2021 aka cafke Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wani malamin addinin Islama da aka fi sani da tsaurara ra'ayi wajen fassara Alkur'ani mai tsauri, a jihar Kano.

An tuhume shi da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW), kuma a watan Disamba 2022, kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, inji rahoton Legit Hausa.

Sheikh Kabara ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa, yana mai cewa koyarwarsa tana da tushe a binciken addini.

Har yanzu dai ana ci gaba da sauraron shari'ar Abduljabbar Kabara, inda ko a watan Mayun 2024 aka sha takaddamar shari'ar a babbar kotu.

A baya bayan nan, Legit Hausa ta rahoto cewa, Sheikh Kabara ya sake sallamar lauyansa, Sadiq Yusuf, matakin da zai iya shafar tafiyar da kararsa.

Abdulazeez Inyass: Malamin Sufanci

An cafke Abdulazeez Inyass, wani malamin darikar Tijjaniyya, a Kano, a watan Mayun 2015 bayan wata huduba da ya yi.

Kara karanta wannan

Muhimman dalilai 4 da suka karya farashin abinci ana shirin azumin Ramadan

An zargi Abdulazee da bayyana cewa Sheikh Ibrahim Niasse, wanda ya kafa Tijjaniyya, ya fi Annabi Muhammad (SAW) girman matsayi.

Rahoton shafin USCIRF ya nuna cewa, a watan Janairun 2016, kotu ta yanke masa hukuncin kisa bayan samun sa da laifin ɓatanci.

Tun daga watan Agusta 2020, ake jiran amincewar gwamnan jihar Kano don aiwatar da hukuncin kisa kan Abdulazeez.

Hukuncinsa ya haifar da suka daga kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, ciki har da Majalisar Turai da kuma USCIRF, waɗanda ke bukatar a sake shi tare da soke dokokin ɓatanci da ke tauye 'yancin ɗan Adam.

Isma'ila Sani Isah: Matashi daga Sokoto

A watan Yulin 2021, aka kama Isma’ila Sani Isah daga jihar Sokoto bisa zargin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a shafinsa na Facebook.

An kama shi ne bayan wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga, inda suke bukatar a ɗauki mataki mai tsauri a kansa, inji rahoton Legit Hausa.

Kara karanta wannan

Adamawa: 'Yan ta'adda sun kai hari babban asibiti, an yi awon gaba da bayin Allah

Duk da cewa an tsare shi, har zuwa Fabrairun 2025, ba a kammala shari'arsa ba.

Majalisar Turai ta nuna damuwa kan ci gaba da tsare shi ba tare da hukunci ba, tare da kira ga a saki shi kuma a soke dokokin ɓatanci da ke cin zarafin 'yancin ɗan Adam.

'Musulunci bai yarda a kashe mai batanci ba'

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Ustaz Abdul-Lateef Adekilekun, shugaban musulman ƙasar Yarbawa ya ce Addinin musulunci bai koyar da kashe wada ya yi kalaman ɓatanci ba.

Ustaz ɗin ya ƙara da cewa duk da haramun ne taɓa martabar Manzon Allah a musulunci amma akwai hanyoyin da Musulunci ya tanada wajen hukunta wanda ya yi ɓatanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel