Yadda Gwamnati Ta Kame Sheikh Abduljabbar, Ta Turashi Magarkama Ya Yi Sallah
- Rahotonni daga jihar Kano sun bayyana cewa, jami'an tsaro sun cafke Sheikh Abduljabbar
- Wannan ya biyo mukabalar da ta gabata a makon jiya, inda aka tumi malamin da abubuwa da dama
- An tsare malamin, inda aka nuna alamar zai yi babbar sallah a magarkama bayan zaman shari'a
Rahotanni da muke samu daga jihar Kano sun tabbatar mana cewa, gwamnati ta kame Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara bisa laifin batanci ga manzon Allah SAW.
Wata sanarwa da kwamishina na yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa hakan ya biyo bayan karbar rahoton farko da aka yi daga ofishin ‘yan sanda daga Ofishin Babban Lauya da kuma kwamishinan shari’a wanda ya shirya tuhuma kan malamin.
KARANTA WANNAN: Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu
Daily Trust ta tattaro sanarwar na cewa:
"Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, babban malamin addinin musuluncin nan dake Kano ya shahara wajen tafsiri mai rikitarwa da maganganun da ake yi wa kallon na batanci ga sahabbai da kuma yin batanci ga Manzon Allah Muhammad (S.A.W) an gurfanar da shi a gaban kotu saboda laifin batanci."
“Wannan ci gaban ya biyo bayan karbar Rahoton Bayanai na Farko daga ofishin 'yan sanda ta Ofishin Babban Lauya kuma kwamishinan shari’a wanda ya shirya tuhumar kan malamin.
“Daga baya an gurfanar da Abduljabbar a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli a gaban Alkalin Kotun Koli ta Shari’a dake Kofar Kudu, Alkali Ibrahim Sarki Yola, inda aka ambaci tuhume-tuhumen da suka hada da batanci, tayar da hankali, da kuma laifuka daban-daban.
"Bayan zaman kotun, ta dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Yuli, yayin da malamin zai ci gaba da zama a hannun 'yan sanda har zuwa ranar Litinin lokacin da za a tura shi gidan yari har zuwa ranar da aka dage karar."
Na janye kalamaina: Abduljabbar ya amince malaman Kano sun yi nasara a kansa
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana cewa, a yi masa afuwa kuma lallai ya janey maganganun da ya yi game Manzon Allah SAW wadanda ake ganin sun taba mutuncin ma'aiki.
A cikin wani sauti karo na biyu da ya aike wa sashen Hausa na BBC ranar Lahadi, malamin ya ce yana fatan "hakan ya zama silar gafara da rahama da jin kai gare ni".
Ya kara da cewa:
"Wadannan maganganu da suka fito daga bakina suka jawo ce-ce-ku-ce game da Ma'aiki SAW, na janye su na kuma janye su."
Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan sautin farko da ya fitar a Lahadin yana neman afuwar wadanda suka fahimci cewa shi ne ya kirkiri kalaman batanci ga Annabi da ake zarginsa da yi.
KARANTA WANNAN: Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu
Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu
A wani labarin, Dino Melaye, tsohon sanata wanda ya wakilci gundumar sanata amajalisar kasa ta takwas, ya kammala karatun digiri na biyu a kan nazarin manufofi daga Jami'ar Abuja.
Tsohon dan majalisar ya bayyana a shafinsa na Facebook a ranar Laraba da yamma, 14 ga Yuli, don nuna murnar sabuwar nasarar da ya samu.
Melaye wanda abokin hamayyarsa na siyasa, Smart Adeyemi ya tsayar da kudirinsa na komawa majalisar dattijai ta tara, ya nuna kwafin sakamakon kammala karatun da jami'ar tarayya ta ba shi tare da taken:
"Daukaka ta tabbata ga Allah har abada."
Asali: Legit.ng