Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

  • A yau Talata, 5 ga watan Afrilu, ne kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 24 kan matashi dan jihar Kano wanda bai yarda akwai Allah ba, Mubarak Bala.
  • Bala dai ya amsa tuhumar da ake masa na yin batanci ga Allah da Manzonsa, Annabi Muhammad
  • Kafin ya zama mara addini, matashin ya yi karatun Al-Kur'ani mai zurfi

Mubarak Bala ya kasance dan Najeriya da ke ikirarin babu Allah kuma shugaban kungiyar wadanda ba su yin addini a Nigeria.

An dai kama Bala kan laifin aikata sabon Allah da cin mutuncin Manzonsa sannan kuma aka gurfanar da shi.

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi
Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi Hoto: BBC Hausa
Asali: Twitter

Matashin ya amsa laifukan da ake tuhumarsa a kai a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu, inda babbar kotun jihar Kano ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 24 a gidan gyara hali.

Kara karanta wannan

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

A nan, Legit Hausa ta tattaro maku wasu abubuwa 10 da yakamata ku sani kan Mubarak Bala:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Bala ya kasance haifaffen dan jihar Kano

2. Ya kasance miji ga Amina Ahmed kuma sun samu haihuwar da daya da shi

3. Ya halarci makarantar firamare na Aliyu Bin Abi Talib wanda wata gidauniyar Musulunci ta kasar Saudiyya ke daukar nauyinta

4. Ya na da burin son ganin ya zama shugaba, a kowane matsayi a matakin tarayya

5. Ya samu horo a akidar Salafanci, sannan ya yi karatun sakandare a makarantar Hassan I Gwarzo da ke Kano, inda ake karatun Qur'ani mai zurfi

6. Bala ya karbi lambar yabo a matsayin gwarzon shekara na kungiyar marasa addini a ranar 8 ga watan Janairun 2021

7. Matashin ya yi suna ne a shekarar 2014 lokacin da rahotanni suka kawo cewa yan uwansa sun kai shi asibitin mahaukata bayan ya fada masu cewa shi bai yarda akwai Allah ba

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari

8. Bayan an sake shi, sai ya zama mai fafutukar kare hakki da nemawa marasa addini a Najeriya yanci

9. An kama Bala a ranar 28 ga watan Afrilun 2020, kan wata wallafa da ya yi a shafin Facebook inda ya ci mutuncin Annabi Muhammad

10. A ranar Talata, 5 ga Afrilu, 2022, Bala ya amsa laifinsa kuma alkali ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari

Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari

Mun kawo a baya cewa kotu ta yanke hukunci kan karar da aka shigar kan Shahararren matashin da ke ikirarin bai yarda da Allah ba, dan asalin jihar Kano, Mubarak Bala, ranar Talata, 5 ga Afrilu, 2022.

Wata babban kotun jihar Kano dake zamanta a Audu Bako Secretariat ta yanke masa hukuncin daurin shekaru ashirin da hudu a gidan gyaran hali bayan amsa laifukan da ake tuhumarsa da su.

Kara karanta wannan

Dalilan Osinbajo na kin yarda Amaechi ya kashe N3.7b wajen tsare hanyar jirgin kasa

Gabanin yanke masa hukunci, Mubarak ya bukaci kotu ta sassauta masa saboda bai aikata abubuwan da ake zarginsa da su ba don tada tarzoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel