Janar Tsiga: Mutane Sun Shiga Firgici sakamakon Sace Tsohon Shugaban NYSC a Katsina
- Mutanen garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina, na ci gaba da alhini kan sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga
- Sace tsohon shugaban na hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), ya sanya tsoro da firgici a zukatan mutanen yankin na Katsina
- Majiyoyi sun bayyana cewa mutane da dama sun yi ƙaura daga gida saboda tsoron da ya shiga zukatansu sakamakon aikin 'yan bindiga
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Sace tsohon shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga da ƴan bindiga suka yi ya sanya mutane a cikin firgici.
Tsoro ya lulluɓe mutanen garin Tsiga da ke jihar Katsina sakamakon sace Maharazu Tsiga da ƴan bindiga suka yi a daren ranar Laraba.

Asali: Twitter
Sace Maharazu Tsiga ya sanya mutane cikin firgici

Kara karanta wannan
'Yan bindigan da suka sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga sun turo saƙo a Katsina
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa sace tsohon shugaban hukumar ta NYSC ya sanya mutane da dama sun tsere daga garin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna da suka tsorata saboda sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga sun fara barin gidajensu saboda gudun afkuwar ƙarin wasu hare-haren.
Wata majiya mai tushe daga yankin, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa tsakanin ranar Alhamis da Juma’a, sama da mutum 400 sun bar yankin.
"Tun daga ranar Alhamis zuwa Juma’a, mutane sama da 400 sun riga sun bar garin. Janar Tsiga babban mutum ne a garin, kuma muna ganin shi a matsayin abin koyi."
“Idan har za a iya sace babban mutum kamar shi haka kawai, to yaya za a yi da talakawa? Wannan ne ya sa mutane suka tsorata, suka fara guduwa daga yankin."
Wani mazaunin yankin da ya bar garin ya ce:
"Dalilin da ya sa muke iya rayuwa a wannan yanki duk da hare-haren ƴan bindiga shi ne kasancewar Janar Tsiga yana nan. Amma yanzu da aka sace shi, wa zai kare mu? Duk wanda ya zauna, to da kansa yake jefa rayuwarsa cikin hatsari."
Ƴan bindiga sun mamayi jama'a
Wani mazaunin garin Tsiga mai suna Abdullahi Rabo ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas sun shiga cikin firgici sakamakon sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga.
Ya bayyana cewa ba zai iya tabbatar da cewa mutane sun bar gidajensu a garin ba saboda yana da faɗi, ta yiwu ko da wasu sun tafi ba za a gane ba.
"Gaskiya abin akwai ban tsoro sace Janar da ƴan bindiga suka yi. Idan har za su iya sace mutum kamarsa lallai dole abin ya zo da firgici."
"Ƴan bindigan sun mamayi jama'a ne shiyasa har suka iya shigowa suka yi wannan ɓarnar, domin da an san da zuwansu da an ɗauki mataki domin mutane su kan fita aikin sintiri."
- Abdullahi Rabo
Ƴan bindiga sun sace ƴan mata
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100
Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun hallaka wani jami'in tsaro tare da yin awon gaba da wasu ƴan mata guda shida a garin Pandogari na ƙaramar hukumar Rafi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng