Dambarwar Albany da Abubuwa 4 da Suka Ta da Kura a Kafofin Sadarwa a Arewacin Najeriya

Dambarwar Albany da Abubuwa 4 da Suka Ta da Kura a Kafofin Sadarwa a Arewacin Najeriya

A yan kwanakin nan kafofin sadarwa sun cika da abubuwan da suka dauki hankali musamman a Arewacin Najeriya wanda al'umma da dama ke tofa albarkacin bakinsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

A kusan lokaci guda abubuwa da dama sun faru kama daga wadanda suka shafi addini da kuma bangarorin zamantakewar rayuwa.

Abubuwa 4 da suka fi jan hankalin al'umma a Arewacin Najeriya
'Qur'anic Convention' da sauran abubuwa da suka tayar da kura a Arewa. Hoto: JIBWIS Nigeria, Amintacciya, Albany TV.
Asali: Facebook

Abubuwan da suka ta da kura a Arewa

'Qur'anic Convention' ne kan gaba wanda ya fi tayar da kura duba da alakar taron da addinin Musulunci da ya rarraba kan malamai kafin daga baya Sheikh Bala Lau ya yi tsokaci a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani, dambarwa kan Cibiyar Darul Hadith na marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albany ta taso a Zaria da ke jihar Kaduna.

Bayan haka, labarin Seaman Abbas Haruna ya taso wanda ake zargin ya sake matarsa da ta sadaukar da rayuwarta lokacin da bai da lafiya.

Kara karanta wannan

Sabon limamin Abuja ya yi nasiha mai zafi ga malamai masu jifan juna ta intanet

Legit Hausa ta duba muhimman abubuwa da suka fi jan hankali a Arewacin Najeriya.

1. Ce-ce-ku-ce kan 'Qur'anic Convention'

Maganar 'Qur'anic Convention' ta ta da kura sosai a kafofin sadarwa inda lamarin ya raba kan malamai.

Shugaban Izalah bangaren Kaduna, Sheikh Bala Lau ya kare matakin shirya taron inda ya ce a shirye suke su karbi gyararraki.

Sai dai wasu malamai daga kowane ɓangare sun soki lamarin da suke ganin bai cikin tsarin Musulunci.

An shirya gudanar da taron ne a ranar 22 ga watan Fabrairun 2025 a Abuja inda za a gayyaci dubban mahaddata Alkur'ani da malamai.

'Qur'anic Convention'

2. Dambarwa kan wakafin Cibiyar Darul Hadith

A yan kwanakin nan, an yi ta ce-ce-ku-ce kan abubuwan da ke faruwa bayan rasuwar Sheikh Muhammad Auwal Albany Zaria.

Sheikh Albany kafin rasuwarsa da bayar da makarantar a matsayin wakafi wanda a yanzu wasu daga cikin 'ya'yansa suke zargin ba a taimakonsu.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

Babban dan marigayin, Abdulrahman Muhammad Adam ya fito ya mayar da martani a shafin Albany TV inda ya ce makarantar ba ta cikin gado kuma tana iya kokarinta wurin taimakon iyalansu.

Ba a dade ba sai ga mahaifiyar wannan bawan Allah ta fito a wani yanayi da ba a ji dadin gani ba.

3. Lamarin Seaman Abbas da Hussaina

Labarin wulakanta Hussaina da ake zargin tsohon soja, Abbas Haruna ya rikita kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya inda aka ce matashin ya sake Hussaina.

Abbas Haruna ya karyata rade-radin cewa ya saki matarsa Hussaina, yana mai cewa suna tare cikin soyayya da zaman lafiya.

Abbas ya tabbatar da cewa matarsa ta kwanta asibiti har tsawon kwanaki 10 amma yanzu ta warke kuma tana shirin komawa gida.

Tsohon sojan ya ce babu wata matsala tsakaninsa da Hussaina kan kudin tallafi, yana zargin wasu ne ke kokarin haddasa rudani a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ji takaicin konewar almajirai, ya ba da umarnin dakile gobara a tsangayu

4. Badalar matashiya yar TikTok a Gombe

Wata matashiya ta tayar da kura inda ta yi wasu bidiyo dauke da kalaman batsa a jihar Gombe wanda ya ja hankalin hukumomi.

Bayan yada bidiyon da ya tayar da hankulan al'umma, hukumar Hisbah a Gombe ta kama yarinyar da kuma mai yi mata bidiyo wanda ake zargin dan daudu ne.

Hukumar Hisbah reshen Kashere a Gombe ta wallafa a shafin Facebook inda ta ce za ta ajiye ta a bangarenta domin ba ta kulawa da kuma sanya ta makarantar Islamiyya saboda gyara mata rayuwa.

Kwamandan Hisbah ya tattauna da Legit Hausa

Shugaban hukumar Hisbah a Gombe, Malam Muhammad Rabi'u ya tabbatar da cewa yarinyar tana hannunsu kamar aka gani.

Amma ya ce yan sanda ne suka kama ta bayan korafe-korafe inda daga bisani rundunar ta mika ta ga Hisbah.

"Bayan wannan yarinya ta yi abin da ta yi, mu abin ya dame mu kwarai ana ta kiraye-kiraye a dauki mataki.

Kara karanta wannan

Jerin manufofin shugaba Tinubu 4 da wasu gwamnoni suka yi fito na fito da su

"Muna shirin daukar mataki aka kira ni a ofishin yan sanda cewa an kama yarinyar da kuma yaron suna bukatar mu tattauna.
"Suna son son damka yarinyar a hannun mu, to ni lokacin ina shirin barin gari sai na tura musu mataimakina inda suka damka yarinyar ga hukumar mu."

- Malam Muhammad Rabi'u

Ya ce a ƙarshe sun tattauna suka ba su yarinyar kuma ta yi nadama, ya ce za su rike ta har zuwa lokacin aurenta.

Kwamandan ya kuma tabbatar da cewa iyayen yaron da aka kama su tare, sun nemi belinsa daga yan sanda amma an ba hukumar Hisbah shi domin a ba shi shawarwari.

5. Farouq Kperogi da Muhammadu Sanusi II

A wani rubutu da ya yi, Farefsa Farouq Kperogi ya yi kaca da Mai martaba Muhammadu Sanusi II saboda wasu kalamai da sarkin ya yi a kan gwamnati.

An ji Sarkin Kano yana cewa ba zai ba gwamnatin Bola Tinubu shawarar da za ta taimake ta ba, wannan ya sa Farfesan ya yi masa kaca-kaca a shafinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da Aminu Ado Bayero, ya ba shi tabbacin kawo karshen matsaloli a Kano

Irinsu Farfesa Ibrahim Bello Kano sun maida raddi amma sai aka koma zargin cewa lamarin ya koma kabilanci, wasu kuma suka ce ramuwar gayya ce.

Ribadu ya kalubalanci Naja'atu kan bidiyon TikTok

A wani labarin, kun ji cewa Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci Naja’atu Muhammad ta janye kalamanta a bidiyon TikTok da ta yi.

Lauyan Ribadu ya ce ya kamata Hajiya Naja’atu ta janye maganganunta kuma ta bayar da hakuri a jaridu guda biyar cikin kwanaki bakwai.

A cikin bidiyon, Hajiya Naja’atu ta zargi Ribadu da goyon bayan gwamnatin Tinubu, wanda a baya ya soka da zargin cewa ya kware a cin hanci a lokacin da yake shugaban EFCC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel