Kudirin Haraji da Abubuwa 9 da Suka Yi wa Gwamnatin Tinubu Illa a Arewacin Najeriya

Kudirin Haraji da Abubuwa 9 da Suka Yi wa Gwamnatin Tinubu Illa a Arewacin Najeriya

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya samu adadin kuri’u masu yawa daga jihohin Arewa a zaben 2023, amma yanzu zancen ya fara canzawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Watanni bayan shiga ofis, farin jinin Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ragu sosai a sakamakon matakan da ya dauka a mulki.

Jaridar Legit Hausa ta duba wasu daga cikin abubuwan da suka bata sunan gwamnatin Bola Tinubu a yankin na Arewacin kasar nan.

Bola Tinubu
Wasu tsare-tsaren Bola Tinubu ba su yi wa Arewa dadi Hoto: Getty Images/@gboyegaakosile
Asali: Getty Images

Abubuwan da suka bata Tinubu a Arewa

1. Cire tallafin fetur da sauran tsare-tsare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasa Bola Tinubu bai kwana a kan karaga ba ya sanar da cire tallafin man fetur wanda a dalilin haka aka samu karin tsadar rayuwa.

Sauran tsare-tsare kamar karya darajar Naira da karin kudin wutar lantarki bai yi wa talakawa musamman na yankin Arewa dadi ba.

2. Sabanin Tinubu da kasar Nijar

Kara karanta wannan

Daga dawowa Najeriya, Tinubu ya shiga yin nade naden mukami a hukumar raya Arewa

Bola Tinubu bai dade da zama shugaban Najeriya a 2023 ba sai sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum a Nijar.

A lokacin shugaban kasar ya fusata, ta kai ya ba sojoji wa’adi su maida mulki ga farar hula a Jamhuriyyar Nijar, amma abin ya faskara.

A sanadiyyar juyin mulkin alaka ta yi tsami tsakanin makwabtan biyu, wannan ya fusata mutanen Arewa da ke kallon Nijar ‘yaruwarta.

3. Nadin mukamai da watsi da ‘yan siyasar Arewa

Da ya fara nada mukamai a gwamnati, an rahoto cewa wasu musamman daga Arewa ta tsakiya sun zargi Bola Tinubu da yin watsi da su.

A lokacin da Abdullahi Adamu ya bar kujerarsa a APC-NWC, mutanen yankinsa sun yi mamakin jin Abdullahi Ganduje ne ya canje shi.

Kin nada Nasir El-Rufai da watsewar kawancen APC da Rabiu Kwankwaso (NNPP) bai taimaka wajen dorewar karbuwarsa a Arewa ba.

4. Wike da kwangilar kasar Israila

Kara karanta wannan

Za a yi aikin sama da Naira Tiriliyan 4 a masarautar Arewa da ta nada Tinubu Jagaba

Tun da Nyesom Wike ya zama Ministan harkokin Abuja, wasu suka fara korafi ganin ba a saba jin ‘dan Kudu ya hau wannan kujera ba.

Ba a kai ko ina ba kuma aka fara tuhumar Ministan da jawo kasar Israila cikin Abuja, wannan lamari ya sa musulmai sun nuna yatsa.

Tsohon gwamnan Ribas ya taimaka wajen karawa Tinubu bakin jini a dalilin rushe-rushensa da yakar masu bara, har lamarin ya je kotu.

5. Zargin yarjejeniyar Samoa

An yi ta yada jita-jita cewa gwamnatin tarayya ta amince da wasu abubuwa da suka saba dokar Najeriya saboda yarjejeniyar Samoa.

Duk da daga baya an fahimci Najeriya ba ta yi na’am da auren jinsi ba, wannan labari maras tushe ya yi wa gwamnatin APC lahani.

6. CBN da dauke ma’aikatu zuwa Legas

Gwamnatin Bola Tinubu ta dauke hedikwatar wasu ma’aikatu kamar FAAN zuwa Legas alhali Abuja ce babban birnin tarayya a kasar tun tuni.

Kara karanta wannan

Yadda goyon bayan kudurin harajin Tinubu ya jawo wa Sanata Barau suka Jibrin a Arewa

Business Day ta rahoto yadda aka dauke wasu ma’aikatan babban bankin CBN daga Abuja zuwa Legas, wannan ya sa zargi ya kara shiga.

7. Zanga-zanga da cafke yaran Arewa

Lokacin da rayuwa ta kara kunci, sai jama’a suka fita zanga-zanga a jihohi da-dama, a maimakon a gyara sai aka ji abin ya kara cabewa.

An cafke wasu da suka fita zanga-zanga, bayan watanni sai aka ga hotunan kanan yaran da aka kai kotu wanda ya jawo suka ta ko ina.

8. Harin Tudun Biri

A karshen shekarar 2023, sojojin Najeriya suka yi kuskuren sakin wuta a garin Tudun Biri, maimakon a kashe miyagu sai aka hallaka jama’a.

Kuskuren da sojoji suka yi a kauyen lokacin maulidi ya bata sunan gwamnatin Tinubu ganin ba a lokacin ne aka fara kashe mutane a haka ba.

9. Kudirin harajin Tinubu

Gwamnatin tarayya ta mika kudiri a majalisa domin canza tsarin haraji a Najeriya, abin da mutanen Arewa suka yi fito na fito da shi.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Barau ya bukaci majalisa ta mayar da sunan Yusuf Maitama a jami'ar FUE

Matsin lambar da aka samu daga malamai, sarakuna, gwamnoni da ‘yan majalisun yankin ya sa dole aka ja baya da zancen tsarin harajin.

10. Alaka da Faransa

Wani abin da yake jawowa shugabancin Tinubu matsala shi ne zargin shisshigewa kasar Faransa wanda ya saba ziyarta da ya karbi mulki.

Ganin yadda kasashen Afrika ke raba gari da Faransa, wasu a Arewa ba su natsuwa da dangantakar da ke tsakanin shugaban da kasar Turan.

An ji cewa akwai masu zargin ana neman kafa sansanin sojojin Faransa a Arewacin Najeriya, zargin da tuni hukumomin kasar suka musanya.

Arewa ta ki yarda da kudirin haraji

Ana da labari cewa Barista Audu Bulama Bukarti ya ce saboda gwamnonin Legas da Ribas suna neman karin kudi a kawo kudirin haraji.

Lauyan da yake kasar waje ya zubo tambayoyin da ya ce kyau a amsa kafin yin na'am da kudirin a majalisa wanda ya nemi ya hargitsa kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng