Shugaba Tinubu, Gwamnoni Sun Yi Ta'aziyyar Uwar Gidan Gwamnan Akwa Ibom

Shugaba Tinubu, Gwamnoni Sun Yi Ta'aziyyar Uwar Gidan Gwamnan Akwa Ibom

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga gwamna Emo Eno bisa mutuwar matarsa
  • Fasto Patience Umo Eno ta kwanta dama ne a ranar Alhamis a wani asibiti da ke jihar Akwa Ibom
  • Shugaban kasar ya ba gwamnan hakuri, tare da yabon kyawawan halayen Misis Patience Emo Eno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Akwa Ibom - Fadar shugaban kasa ta mika ta'aziyyar shugaba Bola Tinubu bisa mutuwar matar gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno.

Patience Umo Eno ta rasa ranta a ranar Alhamis bayan rashin lafiya a wani asibiti da ke jihar, ba a fadi cutar da ta yi ajalinta na.

Kara karanta wannan

Akwa Ibom: Muhimman abubuwa 5 kan matar gwamna da ta rasu

Akwa Ibom
Shugaba Tinubu ya yi alhinin matar gwamnan Akwa Ibom Hoto: Pastor Patience Umo Eno
Asali: Facebook

Sakon ta'aziyyar na kunshe a cikin sanarwar da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yabi yadda ta ke tsayin daka wajen goyon bayan maigidanta a dukkanin al'amuransa da kuma taimakon jama'a.

Gwamnoni sun yi ta'aziyyar matar gwamnan Akwa Ibom

Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar gwamnonin Kudancin kasar nan sun taya gwamna Umo Eno alhinin rashin matarsa, Patience Eno.

A sanarwar da shugaban kungiyar, kuma gwamnan Ondo, Dapo Abiodun ya fitar, an yaba da yadda marigayiyar ta taimakon mijinta kwarai.

An ba gwamna Emo Eno hakurin rashin matarsa

Kungiyar gwamnonin Kudancin kasar nan sun ba gwamnan Akwa Ibom, Emo Eno hakuri bisa rashin mai dakinsa, Patience Umo Eno.

Kungiyar ta ce malamai ba za su iya misalta halin da gwamnan ke ciki ba, inda su ka yi alkawarin karfafa masa gwiwa a wannan lokaci na tsananin alhini.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana bayan mai ɗakinsa ta riga mu gidan gaskiya a wani asibiti

Akwa Ibom: PDP ta yi alhinin rasa Patience Eno

A baya mun kawo labarin cewa jam'iyyar PDP reshen Akwa Ibom ta kadu da mutuwar mai dakin gwamnan jihar, Fasto Patience Umo Eno.

Bayan alhinin da ta taya gwamna Umo Eno, PDP ta kuma dakatar da gangamin yakin neman zaben kananan hukumomin jihar da ake shirin yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.