'Yan Sanda: Yadda Aka Kama Matashiya da Bindigar AK47 Boye a cikin Buhun Gari

'Yan Sanda: Yadda Aka Kama Matashiya da Bindigar AK47 Boye a cikin Buhun Gari

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama Hauwa Yusuf, ‘yar shekaru 30 dauke da bindiga kirar AK-47 ta boye a cikin buhun garin kwaki
  • Rundunar ta bayyana cewa wadda ake zargin, Hauwa Yusuf ta amsa laifin kai makamin ga wani hatsabibin dan bindiga a jihar Katsina
  • An ce kamen na daya daga cikin manyan lamuran da suka faru a cikin watan da ya gabata, inda ‘yan sanda suka kuma kama mutane 2,726

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja- Rundunar ‘yan sanda ta kama wata mata mai suna Hauwa Yusuf, ‘yar shekara 30 da bindiga kirar AK-47 da aka boye a cikin buhun garin kwaki.

Da yake magana yayin faretin wadanda ake zargin a ranar Juma’a a Abuja, kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi, ya ce an kama Hauwa Yusuf ne a kan hanyar Abuja.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sandan Kano ta kadu da karuwar asarar rayuka, an gano dalilai

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan kama mace da bindigar Ak-47 a Abuja
'Yan sanda sun cafke matashiya za ta kai bindiga jihar Katsina. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito Adejobi ya ce wadda ake zargin ta bayyana cewa za ta je jihar Katsina ne domin kai makamin ga wani “hatsabibin dan fashi”.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama matashiya da bindiga a Abuja

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce:

“A hanyar Abuja zuwa Kaduna, mun kama wata Hauwa Yusuf mai shekaru 30, 'yar jihar Katsina, a lokacin da take kan hanyarta daga Nasarawa zuwa Katsina.
“Bayan an bincike ta, an gano bindigar AK-47 guda daya marar lamba, kuma an samu gidajen harsashin bindigar har guda hudu da aka boye a cikin buhun garin kwaki.
“A yayin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa za ta kai sakon ne ga wani hatsabibin dan bindiga da ke addabar jihar Katsina.”

Yan sanda sun cafke masu laifuffuka

Kakakin rundunar ya ce ‘yan sandan sun kama mutane 2,726 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka tare da kwato bindigogi 150 da alburusai 1,788 a cikin wata guda.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

Olumuyiwa Adejobi ya ce rundunar ‘yan sandan ta kuma ceto mutane 207 da aka yi garkuwa da su a lokacin da ake gudanar da bincike, inji rahoton the Punch.

An kama mai kaiwa 'yan bindiga abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan Neja ta yi nasarar kame wani matashi da ke kai kayan abinci ga ‘yan bindiga a dajin jihar.

An kama matashin mai suna Ibrahim ali da aka fi sani da Bajala bayan kama wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne a yankin Lambata a karamar hukumar Gurara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.