Rundunar 'yan sanda sun cafke mutane 101 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka
- Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta bayyana nasarar da tayi na kama mutane 101 da ake zargi da aikata wasu manyan laifuffuka a faɗin jihar
- Daga cikin laifuffukan da ake zargin mutanen da aikatawa akwai; garkuwa da mutane, satar ababen hawa da kuma shaye-shaye
- 'Yan sandan sun sami wannan gagarumar nasarar ne tun bayan kama aikin sabon kwamishinan 'yan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta bayyana kama mutane 101 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka tun bayan kama aikin sabon kwamishinan 'yan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko.
Sabon kwamishinan 'yan sandan yace:
"Waɗanda aka kama sun haɗa da; 'yan fashi da makami 27, masu garkuwa da mutane 14, masu zamba cikin aminci shida."
KARANTA ANAN: Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta
"Sauran sune, mutane uku masu ta'amali da miyagun ƙwayoyi, ɓarayin motoci biyar, da kuma yan tada zaune tsaye su 46," a cewarsa
Kwamishinan 'yan sandan da jami'ansa sun kuma kwato abubuwa daga hannun waɗan da ake zargin, kamar yadda Thenation ta ruwaito.
Daga cikin abubuwan da suka ƙwato akwai bindigogi guda shida harda ƙirar AK-47.
KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun afka makarantar firamare a Kaduna, sun kwashe dalibai da Malamai
Haka zalika 'yan sandan sun ƙwato motoci 16, keke nafef guda uku, mashin guda tara, wuƙaƙe guda 36, da kunshin ganyen wiwi, katan 57 na maganin 'Diclofenac', da kuma talabishin guda ɗaya.
Kwamishin yace: "A ƙoƙarin da muke yi yadda yakamata, mun cigaba da aiki kafaɗa-da kafaɗa da sauran hukumomin tsaron jihar Kano domin kawo karshen, ta'amali da miyagun ƙwayoyi, da kuma kawar da 'yan daba."
A wani labarin kuma Hukumar Kiyaye Haɗurra Ta Ƙasa Ta Kama Masu Laifi 10,455 A Cikin Watanni Biyu
Shugaban hukumar reshen jihar Lagos, Mr Olusegun Ogungbemide, ya bayyana haka a wata fira da ya yi da NAN.
Ya kuma ƙara da cewa hukumar zata cigaba da gudanar da aikinta a jihar yadda yakamata musamman a manyan hanyoyi.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77
Asali: Legit.ng