Hauwa Yunus: Labarin yar shekara 24 da ke garkuwa da mutane wacce ke yaudarar maza da kyawunta

Hauwa Yunus: Labarin yar shekara 24 da ke garkuwa da mutane wacce ke yaudarar maza da kyawunta

- Yan sanda sun kama wata matashiya mai suna Hauwa Yunus, wata gawurtaciyyar mai garkuwa da mutane a Abuja

- An tattaro cewa matashiyar mai shekara 24 wacce ke zama a jahar Nasarawa na amfani da kyawunta wajen yaudarar maza har su fara soyayya sannan daga bisani ta yi garkuwa da su don kudin fansa da taimakon tawagarta

- A yanzu haka Hauwa na ba yan sanda hadin kai waje gano tawagar masu garkuwa da mutane a yankin arewacin kasar

Yan sanda sun kama wata matashiya mai suna Hauwa Yunus wacce aka alakanta da lamarin garkuwa da mutane daban-daban a Abuja.

An tattaro cewa matashiyar mai shekara 24 ta fallasa wa yan sanda yadda ta ke amfani da kyawunta wajen yaudarar maza har su fara soyayya sannan daga bisani ta yi garkuwa da su da taimakon tawagarta don karban kudin fansa, PM News ta ruwaito.

Hauwa Yunus: Labarin yar shekara 24 da ke garkuwa da mutane wacce ke yaudarar maza da kyawunta
Hauwa Yunus: Labarin yar shekara 24 da ke garkuwa da mutane wacce ke yaudarar maza da kyawunta
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Hauwa na zama a kauyen Masaka da ke jahar Nasarawa kuma ta yi aure sau uku. Ta kasance yar asalin jahar Jigawa.

Hauwa ta kuma fallasa cewa ta yi garkuwa da wata kawarta don kudin fansa. Daga bisani sai kawar tata ta mutu sakamakon raunin da ta ji a horon da masu garkuwan suka yi mata yayinda Hauwa ta sace dukkanin kayayyakinta.

Matashiyar wacce ta kuma kasance yar kwaya ta bayyana cewa ta sha yiwa wadanda ta sace fyade.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu mutanen Borno na son Buhari – Fadar shugaban kasa

Hauwa wacce tawagar sufeto janar na yan sanda karkashin jagorancin Abba Kyari suka kama a Abuja, na ba yan sanda hadin kai wajen gano masu garkuwa da mutane a wasu yankunan kasar.

A baya mun ji cewa rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun kama wasu mutane biyu a karamar hukumar Fika da ke jihar Yobe, da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga Jaridar Daily Trust, Jami’an tsaro sun kama wadannan mutane ne a lokacin da su ke kokarin karbar kudin fansa.

Jaridar ta ce wadanda ake zargin sun shiga ragar ‘Yan Sanda ne yayin da su ke yunkurin karbar kudi N500, 000 daga Iyalin wasu da su ka yi wa ta’adi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel