Gwamnati Ta Hana Amfani da Lasifika a Masallatai da Coci, an Kafawa Masu Ibada Sharadi
- Gwamnatin Enugu ta sake daukar matakai na magance matsalar gurbacewar sauti a fadin jihar yayin da ta gana da shugabannin addinai
- Gwamnatin ta ba shugabannin Musulmai da Kirista wa'adin kwanaki 90 da su tabbatar an cire lasifikun da ke wajen masallatai da majami'u
- Hakazalika, gwamnatin ta ce dole masallatai da majami'u su sanya makarin fitar sauti waje domin magance korafe-korafen jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Enugu - Gwamnatin Enugu ta ba dukkanin masallatai da majami'un da ke fadin jihar wa'adin kwanaki 90 da su cire duk wata lasifika da ke a wajen wuraren ibadarsu.
Gwamnatin ta kuma umarci shugabannin masallatai da coci na jihar da su sanya matakan kariya a cikin wuraren ibadunsu domin hana sauti fita waje.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an cimma wannan matsayar ne a ranar Alhamis, yayin wata tattaunawar masu ruwa da tsaki da shugabannin addinan biyu da kuma gwamnatin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta hana amfani da lasifikar waje
Rahoton ya ce gwamnati ta kira wannan taron ne yayin da take kokarin aiwatar da shirinta na yaki da gurbacewar sauti a fadin jihar.
Taron na hadin gwiwa da hukumar raya babban birnin Enugu ta shirya ya samu halartar shugabannin Musulmai da na Kirista, masu aikin yada labarai da jami’an gwamnati.
Bayan taron, shugaban hukumar raya babban birnin Enugu, Uche Anya, ya bada wa'adin ga shugabannin addinai da su tabbatar an cire kowace lasifika, inji rahoton SaharaReporters.
Gwamnati na yaki da gurbataccen sauti
A cikin 2023 ne gwamnatin jihar ta umarci dukkanin gidajen rawa, mashayar giya, da sauran gidajen nishadi da su rage gurbata sauti a babban birni, musamman a unguwannin jama'a
Da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a wajen taron, Mista Anya, ya ce gurbacewar sauti ya zama babban kalubale ga jihar.
Ya nuna damuwarsa kan yadda ofishinsa ya karbi koke sama da 1,000 kan yadda sautin majami’u, masallatai da wuraren kasuwanci ya ke zama hayaniya ga gidajen jama'a.
Ramadan: Magidanci ya fasa lasifikar masallaci
A wani labarin, mun ruwaito cewa zuciyar wani magidanci ta kai har wuya inda ya garzaya masallacin anguwarsu a fusace, ya fasa lasifikar waje.
An ce mutumin ya aikata hakan ne sakamakon hana shi barci da sautin lasifikar ke yi a yayin da ake sallar dare a lokacin watan Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng