Sharaɗi 15 da Gwamnatin Tarayya ta shata wa wuraren bauta a Najeriya

Sharaɗi 15 da Gwamnatin Tarayya ta shata wa wuraren bauta a Najeriya

- Kada a haura awa daya a wuraren bauta

- Dole ne a sanya alamomin kiyaye dokar kare kai a wuraren bauta

- Babu zuwa makarantun Islamiya, Tahfizu, ko makarantun dare

A ranar Talata ne Gwamnatin Tarayya ta fitar da sharuɗan bude wuraren bauta a fadin kasar domin ci gaba da gudanar da ibadu.

Babban jami'i a kwamitin kar da kwana kan cutar korona na kasa, Sani Aliyu, ya ce duk da an sassauta dokar kulle ta bude wuraren bauta, ya fi aminci mutane su yi ibadarsu a gida

“Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar sake bude wuraren bauta tare da shata wasu ka'idoji na musamman, amma idan zaku iya yin ibadunku a gida, to hakan sai ya fi aminci."

"Zai fi kyau mu kasance a gida yayin gudanar da ibada fiye da zuwa wurin bauta, domin samun aminci da gudun kamuwa da cutar korona."

"A yayin la'akari da yadda cutar korona ke ci gaba da yaduwa, yana da muhimmanci wuraren bauta su gudanar da al'amuransu cikin aminci don tabbatar da kare lafiyar al'umma."

"A sanadiyar haka, mun tsara wannan ka'aidodi da sharuɗan da dole sai an kiyaye a wuraren bauta da ke fadin kasar nan."

Sani Aliyu
Sani Aliyu
Asali: Twitter

"Mun tsara ka'aidodin ne tare da jagorancin shugabannin addinai na kasar, kuma ya kamata a yi amfani da su wajen gudanar da al'amura a wuraren bauta."

A cewarsa, duba da yanayi na taron jama'a da yawa a majami'u, wuraren ibadu su na da hadarin yaduwar cutar korona a tsakanin masu bauta.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta zaftare kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi

Ya ce: "Don haka wuraren bauta da ba su da ikon kiyaye wannan ka'idodi, kada kowace gwamnatin jiha ta ba su damar bude wurin bautarsu."

Aliyu ya ce dole ne dukkanin wuraren bauta su amince da wannan sharuɗa da aka shata da manufar tsare lafiyar al'umma.

Cikin sharuɗan da ya wassafa sun hadar da samar da ruwa mai gudana da sabulun wanke hannu, da kuma sunadarin tsaftace hannu (Sanitizer), a mashiga da mafita ta kowane wurin bauta.

Sauran sharuɗan sun hadar da:

Babu taron jama'a gabani ko bayan an kammala ibada.

Tsaftace wuraren bauta akai-akai da sunadarai masu kashe kwayoyin cututtuka.

Ana son a dinga daukan sunayen duk mutanen da suka shiga wuraren bauta domin gudanar da ibada.

Dole masu bauta su rika amfani da takunkumin rufe fuska.

Ba a son mutane su rika gaisawa da juna, sumbata, ko rungumar juna.

Kada a rika cudanya wajen amfani da abin shimfida daya yayin gudanar da ibada. Kuma a rika ba da tazara da juna ta tsawon mita biyu.

A sanya alamomin tunatar da mutane a kan yin nesa-nesa da juna, kuma mutanen da suka fito daga gida su kasance a tare da juna.

An saya masu lura da an kiyaye ka'idoji a wuraren bauta, sai dai kada a bari wadanda suka haura shekaru 55 zuwa sama su yi wannan aiki na lura.

An bai wa coci damar budewa daga karfe 5.00 na safe zuwa 8.00 na Yamma.

Kada kowace ibada a coci ta haura ta tsawon awa daya, tare da bayar da tazara ta minti 30 gabanin wasu masu bautar su sake shiga domin a samu damar tsaftace cocin.

Ana son iska ta wadata saboda haka dole a bude kofa da tagogi a duk lokacin gudanar da ibada a wuraren bauta.

Za a bude masallatai minti 15 gabani da kuma minti 10 bayan kowace sallah (minti 25 kenan).

Kada gaba daya lokacin sallar Juma'a ya haura awa daya.

Makarantun Islamiya, Tahfizu, da Makarantun dare za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Ana shawartar mutane masu rauni da suke da wasu cututtukan kamar ciwon suga da ciwon zuciya, su gudanar da ibadunsu a gida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel