Wani mutumi ya fasa lasifikar masallaci, saboda tana hana shi bacci a watan Ramadana

Wani mutumi ya fasa lasifikar masallaci, saboda tana hana shi bacci a watan Ramadana

- An kama wani mutumin kasar Indonesiya bisa zargin farma wani masallaci da kuma lalata na’urar lasifika

- Mutumin yayi korafin cewa masallacin na damunsa da hana shi bacci a lokacin watan Ramadan

- Masallacin dai kan gudanar da tafsirin Al-Qur’ani, wanda take amfani da lasifika wajen isar da sakon, cikin dare har zuwa wayewar gari a lokacin Ramadan

Rahotanni sun kawo cewa an kama wani mutumin kasar Indonesiya bisa zargin farma wani masallaci da kuma lalata na’urar lasifika, sakamakon cewa da yayi masallacin na damunsa da hana shi bacci a lokacin watan Ramadan.

A lokacin Ramadan, masallacin kan gudanar da tafsirin Al-Qur’ani, wanda take amfani da lasifika wajen isar da sakon, cikin dare har zuwa wayewar gari.

Wani mutumi ya fasa lasifikar masallaci, saboda tana hana shi bacci a watan Ramadana
Wani mutumi ya fasa lasifikar masallaci, saboda tana hana shi bacci a watan Ramadana
Asali: Depositphotos

A ranar Lahadi da misalin karfe 3:00 na tsakar dare, mutumin wanda ke da zama a kusa da masallacin, ya farma masallacin a lokacin tafsiri rike da adda, inda ya tarwatsa taron jama’a daga cikin masallacin sannan ya lalata lasifikar.

KU KARANTA KUMA: An kai farmaki sakatariyar APC, an sace takardu, na’urar sanyaya wuri, talbijin da sauransu

A lokacin da aka gurfanar dashi, Ns ta fada ma hukumomin cewa ya dauki matakin ne yan kwani bayan ayyukan masallacin sun hana shi bacci tsawon wasu kwanaki.

“Har yanzu muna kan tambayar mai laifin,” Shugaban yan sandan Meulaboh Budi Eka Putra ya bayyana a lokacin da manema labarai suka tuntube shi akan ci gaban lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel