Gwamnatin Rwanda ta haramta kiran Sallah a masallatai
- Birnin Kigali, babban virnin Rwanda yai kowanne birni kyau a Afirka
- Gwamnatin kasar ta haramta coci da masallatai saboda suna damun muutane yayin bacci ko hutawa
- A kasashe da dama ana samun karuwar wuraren ibada musamman masallatai ta coci-coci
A wani mataki da ka iya jawowa gwamnatin kasar bakin jini, an haramtawa masallatai a kasar Rwanda kiraye-kirayen sallah a lasifika, inda gwamnatin ta kira lamarin da bata iska, watau Noise Pollution wai don mutane na cewa an dame su.
Matakin na zuwa ne bayan da aka rushe akalla coci 700 a fadin babban birnin kasar, inda shugaban kasar Paul Kagame yace yana mamakin yadda suka basu a kasar kuma basu baiwa jama'ar kasar koda ruwan burtsatsai.
DUBA WANNAN: Zamu dawo da yan matan Dapchi, Buhari ya fadi a Yobe
Kungiyoyin addinai dai sunyi alla-wadai da matakin da karamar kasar ta tsakiyar Afirka ta dauka inda suka ce matakan na tauye hakkin jama'a na bin addinan da suke so.
A 1994, kasar ta Rwanda ta tsunduma yakin basasa inda taga kisan gilla na kabilanci wanda ya salwantar da akalla 800,000 daga kananan kabilun kasar (Tutsi) wanda manyan kabilu kasar suka shirya, (watau Hutu).
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng