Gwamnatin Edo Za Ta Rufe Cocina, Masallatai, Gidajen Rawa Da Basu Da Abun Hana Jin Karar Sauti

Gwamnatin Edo Za Ta Rufe Cocina, Masallatai, Gidajen Rawa Da Basu Da Abun Hana Jin Karar Sauti

  • Daga yanzu za a dunga rufe cocina, masallatai, wuraren taro, gidajen rawa da sauran kasuwanci masu alaka a jihar Edo idan har ba su saka abun daidaita karar sauti ba
  • Gwamnatin jihar Edo ta sanar da cewar an bayar da sanarwar kwanaki 90 ga mamallakan wadannan wurare
  • An tattaro cewa wa'adin da aka diba kan haka zai cika a ranar Juma'a, 31 ga watan Maris

Edo - Gwamnatin jihar Edo ta ba cocina, masallatai, wuraren taro, gidajen rawa da sauran cibiyoyin jama'a da basu saka abun daidaita karar sauti a wurarensu ba wa'adin yin hakan.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa gwamnatin ta ce wa'adin cike ka'idoji kan gurbatar hayaniya zai cika ne a ranar Juma'a, 31 ga watan Maris.

Gwamnan jihar Edo
Gwamnatin Edo Za Ta Rufe Cocina, Masallatai, Gidajen Rawa Da Basu Da Abun Hana Jin Karar Sauti Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

An sanar da wannan matsaya da wa'adin ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana tsakanin jami'an gwamnati da mamallakan wuraren da ke bukatar a daidaita hayaniyarsu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan Jihar Da PDP Ke Mulki Zai Rufe Masallatai Da Coci-Coci A Jiharsa, Ya Bada Dalili

Legit.ng ta tabbatar da cewar tawagar hadin gwiwa daga ma'aikatun tsare-tsare,raya birane da yanki da kuma ma'aikatar muhalli sun mika takardar sanarwa ga mamallakan wadannan cibiyoyi da kasuwanci da su ba umurnin gwamnati hadin kai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnatin jihar ta bayyana a wata sanarwa cewa:

"An dauki wannan mataki ne bayan taron masu ruwa da tsaki da aka yi tsakanin jami'an gwamnati da mamallakan wadannan wurare da ke bukatar a daidaita hayaniyarsu, wanda aka yi a ranar 31 ga watan Oktoban 2022. Kuna bukatar abun daidaita karar sauti a wurarenku."

Mun tura takardar sanarwa ga wadanda abun ya shafar - Gwamnatin Edo

Bugu da kari, kwamishinan MPPHURD, Isoken Omo ya ce sanarwar ya kuma lissafa wasu matsaya da aka cimma tsakanin masu ruwa da tsaki da gwamnati kan ba wa'adin hadin kai, rahoton Punch.

Da yake ci gaba da martani ga sanarwar, Isoken Omo ya ce:

Kara karanta wannan

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Daga Dr Sani Rijiyar Lemo

"Mamallakan wuraren na da wa'adin kwanaki 90. Sanarwar na kuma dauke da bayani kan irin abubuwan daidaita sauti da za a yi amfani da su da kuma rawar ganin da ma'aikatar muhalli za ta taka wajen samar da karin bayani kan abun hana fitar karar saui da ake bukata."

A wani labari na daban, yan Najeriya da dama sun nuna fushinsu bayan bayyanar wani bidiyo da ake bushasha da bandir-bandir din sabbin kudi a wajen wani biki yayin da talakawa ke nemansu ruwa a jallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel