Abubuwa 13 da mafi yawan Musulmai da Kirista ba su sani ba game da Yesu Kiristi

Abubuwa 13 da mafi yawan Musulmai da Kirista ba su sani ba game da Yesu Kiristi

- Robin Scott ya ce ya gano abubuwa 13 wanda suke da dagantaka da juna a addinin kirista da na musulmi

- Musulmai ‘yan Nijeriya sun jawo hankalin al’umman musulmi maza da mata da a saurari abin da Robin Scott ya ce ya gano

- Scott ya ce babu bambanci mai yawa tsakanin addinin Kirista da na Musulunci

Robin Scott ya bayyana abubuwa 13 wanda ya gano kan Yesu Almasihu, a game da addinnin Musulunci da kuma Kristanci, kamar yadda aka rubuta a cikin Alƙur'ani mai tsarki da kuma littafi mai tsarki wato Bible.

Kamar yadda Legit.ng ta samu daga shafin Nijaloveinfo, Bayan Scott ya bayyana wadannan abubuwa 13 zai musulmai ‘yan Nijeriya suka jawo hankalin al’umman musulmi maza da mata da a saurari abin da Robin Scott. ya ce.

Abubuwa 13 da mafi yawan Musulmai da Kirista ba su sani ba game da Yesu Kiristi
Littafi masu tsarki

Scott ya ce babu bambanci mai yawa tsakanin addinin Kirista da na Musulunci.

1. Yesu ya koyar da cewa Allah daya ne, kuma Allah ne kaɗai ya kamata a bauta kamar yadda ya koyar a Deut 6: 4, Mark 12:29. Musulmai kuma sun yi imani da wannan kamar yadda Alƙur'ani ta koyar a aya 4: 171.

2. Yesu bai ci naman alade, kamar yadda aka koyar a cikin Bible Leviticus 11: 7, haka ma musulmai kamar yadda Alkur'ani ta koyar a aya 6: 145.

3. Yesu na amfani da kalmomin "As salaamu Alaykum" wato aminci ya tabbata a gare ka kamar yadda za a samu a cikin Yahaya 20:21. Musulmai kuma na sallama da juna ta wannan hanya.

4. Yesu ya ce ko wane lokaci cewa " Da yada Allah" (Inshallah), musulmai ma na amfani da kalman kafin yin wani abu kamar yadda Alkur'ani ta koyar a yoyi 18: 23-24.

5. Yesu na wanke fuskarsa, hannayensa da kafafunsa kafin yin addu'a. Musulmai na yi wannan.

6. Yesu da kuma sauran annabawan littafi mai tsarki wato Bible na yin addu'a tare da yin sujjada (kai zuwa ga ƙasa) kamar yadda za a samu a cikin Matthew26: 39. Musulmai na sujjada kamar yadda Alkur'ani ya koyar a cikin aya 3:43.

7. Yesu ya bar gemu kuma yana sa throbe. Wannan kuma Sunnah ne ga duk musulmai da ya yi hakan.

8. Yesu ya bi doka, kuma ya yi imani da dukan annabawa, za a iya samu a Matiyu 5:17. Musulma ma haka kamar yadda Alkur'ani ta koyar a ayoyi 3:84, da kuma 2: 285.

9. Uwar Yesu Maryam tana saka tufafin zai rufe jikinta gaba daya da kuma saka gyale wato hijabi kamar yadda aka samu a 1 Timothawus 2: 9, Genesis 24: 64-65, da kuma Korantiyawa 11: 6. Musulmai mata ma zuna rufe jikinsu kamar yadda Alkur'ani ta koyar a ayar 33:59.

10. Yesu da kuma sauran annabawan littafi mai tsarki duk sun yi azumi har zuwa kwanaki 40 kamar yadda yake a cikin Exodus 34:28, Daniel 10: 2-6. 1Kings 19: 8, da Matiyu 4: 1. Musulmai ma na yin haka a cikin watan na Ramadan. An bukaci kowani musulmi da ya yi azumin kwana 29 ko 30 wanda aka wajabta a cikin Al’kur'ani 2: 183.

KU KARANTA: Shaikh Zakzaky ya raba abinci ga mabukata don Ramadana a Zariya (Hotuna)

11. Yesu yana cewa : "Aminci Allah zuwa wannan gidan" a duk lokacin zai shiga, Luka 10: 5, da kuma gaishe da mutane da yin sallama kamar: "Amincin Allah ya tabbata a gare ku". Musulmai yi daidai da abin da Yesu ya yi, kamar yadda aka koyar a cikin Alkur'ani ayar 24:61.

12. An yi wa Yesu kaciya. Ita kaciya ta kasance 1 cikin fitrah 5 a musulunci, don haka an bukaci musulmi maza a yi musu kaciya. Bisa ga littafi mai tsarki, a cikin Luka 2:21, Yesu yana da kwana 8 sa'ad nan aka yi masa kaciya. A cikin Kur'ani aya 16: 123 an bukaci duk musulmi da su bi akidar Annabi Ibrahim. Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce: " Annabi Ibrahim ya yi wa kansa kaciya lokacin da yake shekaru 80."

13. Yesu yana magana da harshen Aramaic da kuma kira Allah "Elah", wanda aka sani a matsayin "Allah". "Elah" da harshen Aramaic da kuma "Allah" a harshen Larabci duk daya ne.

An samu "Elah" daga Larabci "Allah", kuma tana nufin "ALLAH". "Allah" a harshen Larabci kuma yana nufin "ALLAH".

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa

Asali: Legit.ng

Online view pixel