Da Ɗuminsa: Annobar Amai Da Gudawa Ta Kashe Mutane 7 a Gombe
- An samu ɓullar annobar amai da gudawa a jihar Gombe inda ta hallaka mutum 7
- Kwamishinan lafiya na jihar Gombe Dr Habu Ɗahiru ya tabbatar da ɓullar annobar
- Ya ce an yi wa mutane 32 da suka kamu magani an kuma sallame su yana mai shawartar mutane su rika amfani da ruwa mai tsafta
Annobar amai da gudawa ta salwantar da rayukan mutane bakwai yayin da wasu suna nan suna jinya a cibiyar lafiya ɓai ɗaya, PHC, da ke mazabar Garko a ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe, Daily Trust ta ruwaito.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Habu Ɗahiru, cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ya ce tawagar bada taimakon gaggawa ta tabbatar da annobar tare da kafa cibiyar jinya a Bogo Model PHC.
DUBA WANNAN: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi
A cewarsa, an tura tawagar ne sakamakon rahoton da aka samu kan bullar cutar da ake zargi amai da gudawa ne da rasuwar yaro ɗan shekara biyu a kauyen a Kalajanga da ke Akko, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Ya ce cikin kwanaki bakwai da suka gabata, an yi wa mutane 32 magani a cibiyar jinyar an sallame su.
A cewarsa, shan gurɓataccen ruwa ne ya janyo ɓullar annobar.
"An saba samun ɓullar amai da gudawa a farkon damina.
KU KARANTA: An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Ƴan Bindiga Aiki a Katsina
"Don haka yana da saurin yaɗuwa a garuruwa idan ba a ɗauki matakan daƙile shi ba," in ji shi.
Kwamishinan ya shawarci mazauna jihar su rika amfani da ruwa mai tsafta wurin sha, girki da tsaftace muhallinsu.
A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.
Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".
Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.
Asali: Legit.ng