Annobar amai da gudawa ta halaka mutane 526 a jihohi 18

Annobar amai da gudawa ta halaka mutane 526 a jihohi 18

  • Hukumar ta bayyana cewa annobar amai da gudanawa ta halaka mutane 526 a kasar daga watan Junairu zuwa yanzu
  • A cewar hukumar da ke yaki da hana cutuka masu yaduwa lamarin ya shafi jihohi 18 iki har da babbar birnin tarayyar kasar wato Abuja
  • Sai dai kuma ta bayyana cewa an samu ragowar wadanda suka kamu da cutar a makonni biyu da suka gabata

Hukumar da ke yaki da hana cutuka masu yaduwa ta kasa ( NCDC), ta bayyana cewa annobar kwalara ta kashe mutane 526 a kasar daga watan Junairu zuwa yanzu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Talata, 27 ga watan Yuli. Ta kuma bayyana cewa lamarin ya shafi jihohi 18 ciki har da birnin tarayya Abuja.

Annobar amai da gudawa ta halaka mutane 526 a jihohi 18 har da Abuja
Annobar Kwalara ta halaka mutane 526 a Najeriya Hoto: Unicef.org
Asali: UGC

Sashin Hausa na BBC ya ruwaito cewa NCDC ta ce kashi 28 cikin 100 na wadanda suka kamu da annobar duk kananan yara ne da ke tsakanin shekara biyar zuwa 15.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta

Har ila yau kashi 51 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar amai da gudawar sun kasance maza ne, yayin da aka samu kashi 49 suka kasance mata.

Hukumar ta ce cikin makwanni biyu da suka gabata, an samu raguwar sabbin wadanda suka kamu da cutar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jihar Bauchi na da mutum 2438, sai Kano 674, Filato 87, idan aka kwatanta da kafin wannan lokacin.

Hankula sun tashi sosai yayin da yawan wadanda suka mutu sakamakon kwalara ya yi muni a Abuja

A gefe guda, mun ji a baya cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar kwalara a Babban Birnin Tarayya (FCT) ya haura 60, kamar yadda karamar Ministar Abuja, Dakta Ramatu Tijjani Aliyu, ta bayyana.

Cutar kwalara ta fara ɓarke ne a cikin karamar Hukumar Abuja a ranar 23 ga Yunin 2021, inda ta kashe aƙalla mutum bakwai daga cikin 91 da ake zargi sun kamu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hankula sun tashi sosai yayin da yawan wadanda suka mutu sakamakon kwalara ya yi muni a Abuja

Aliyu, ta tabbatar da adadin mutanen da suka mutu a ci gaba da wayar da kan al’umma kan cutar kwalara da sauran munanan cututtukan gudawa da suka barke a yankunan Pyakasa da Gwagwa a cikin babban birnin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel