Gidauniyar musulunci ta dauki nauyin yi wa mutane 250 tiyata kyauta a asibitin Aminu Kano

Gidauniyar musulunci ta dauki nauyin yi wa mutane 250 tiyata kyauta a asibitin Aminu Kano

- Gidauniyar musulunci ta dauki nauyin yi wa mutane 250 tiyata kyauta a asibitin Aminu Kano

- Gidauniyar dai daga kasar Sudan mai suna Patients Helping Fund Sudan

- A gobe ne dai likitocin za su fara aikin tiyatar gadan-gadan ga marasa lafiyar.

Labaran da suke zuwa mana na nuni da cewa wata gidauniyar tallafawa marasa lafiya ta musulunci daga kasar Sudan mai suna Patients Helping Fund Sudan a turance zata dauki nauyin yiwa marasa lafiya kimanin 250 tiyata kyauta a asibitin Malam Aminu Kano.

Gidauniyar musulunci ta dauki nauyin yi wa mutane 250 tiyata kyauta a asibitin Aminu Kano
Gidauniyar musulunci ta dauki nauyin yi wa mutane 250 tiyata kyauta a asibitin Aminu Kano

KU KARANTA: Tambuwal na fuskantar matsin lamba ya kalubalanci Buhari a 2019

Tawagar likitocin da za suyi tiyatar dai tuni sun iso Najeriya tun ranar asabar din da ta gabata inda kuma jiya Lahadi suka kammala rangadin kayayyakin aikin da za suyi anfani da su wajen yin tiyatar yau kuma tuni suka fara gyarawa tare da shirya marasa lafiyar da za suyi wa aikin.

Legit.ng dai ta samu cewa a gobe ne dai likitocin za su fara aikin tiyatar gadan-gadan ga marasa lafiyar.

Haka ma dai ana sa ran likitocin za su yi wa ajin marasa lafiya kimanin 5 aikin da jimillar su ya kai 250 dai dai.

A wani labarin kuma, Shugaban babbar asibitin tarayya dake a garin Keffi na jihar Nasarawa mai suna Dakta Giyan Joshua Ndom ya tabbatar da cewa asibitin sa na kan binciken wasu marasa lafiya su uku da ake zargin sun kamu da cutar nan ta masassar Lassa.

Dakta Joshua yayi wannan kalamin ne yau Alhamis a garin na Keffi yayin da yake zantawa da manema labarai game da lamarin.

Legit.ng ta samu cewa haka zalika hukumar asibitin tuni har ta kebe wadanda ake zargin sannan ta kuma aike da jinin su zuwa a dakunan gwaji domin tabbatar da lafiyar mutanen.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng