Matasa 72 ne suka haukace a Zamfara sakamakon shan miyagun kwayoyi

Matasa 72 ne suka haukace a Zamfara sakamakon shan miyagun kwayoyi

- Kamar yadda Mista Ladan ya ce, an fi samun shaye-shayen miyagun kwayoyin ne tsakanin al'umma masu shekaru 9 - 39, kuma sun fi shan kwayoyi kamar su Tramadol, Rafenol da suaran su

- Ya kuma ce shaye-shayen yana kara yawaita tsakanin yan mata da matan aure musamman wandanda suke makarantun gaba da sakandare

- Mista Ladan ya ce hukumar ta NDLEA, tare da hadin gwiwa da malaman addini, masu sarautun gargajiya da wasu kungoyin matasa sun iya kokarin su domin fadakar da al'umma kan ilolin shaye-shayen

Kimanin matasa maza da mata 72 ne suka sami tabin hankali a dalilin ta'amulli da miyagun kwayoyi cikin shekaru uku da suka wuce a jihar Zamfara. Wannan zancen ya fito ne daga bakin babban jami'in ma'aikata na hukumar Yaki da masu ta'amuli da miyagun kwayoyi (NDLEA), Mista Ladan Hashim.

Mista Ladan ya fadi wannan magana ne a wata hira da akayi da shi cikin wata shiri mai suna 'Ya muka Kwana' a gidan Rediyon Pride FM da ke Gusau. Ya kara da cewa adadin matasa da maza da mata da ke shaye-shayen miyagun kwayoyi ya kai halin ha'ula'i kuma ya zama dole a dauki matakin dakatar da shi.

Matasa maza da mata 72 ne suke fama da tabbin hankali cikin shekaru 3 a Zamfara
Matasa maza da mata 72 ne suke fama da tabbin hankali cikin shekaru 3 a Zamfara

"Galibi an fi samun shaye-shayen cikin al'umma masu shekaru 9 - 39, kuma sun fi shan kwayoyi kamar Tramadol, Rafenol da sauran su, wasu lokutan ma suna shan kwayoyi daban-daban a lokaci daya. Wadanan kwayoyin na da matukar illa ga lafiyan su," inji shi.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta shiga cikin maganar zargin da Hukumar Soji ta yi wa wani soja na cewar shi dan Boko Haram ne

Ya kuma koka kan yadda yan mata da matan aure musamman wanda ke makarantun gaba da sakandare suke shan magungunan tari na ruwa, har ma ya bayar da labarin wata matashiya da ta koya wa mahaifiyarta shan kwayan.

A cewarsa, wadanda suka samun tabin hankalin suna Asibitin Kwakwalwa na garin Anka domin karban magani, ya yi kira ga iyaye su sa ido kan 'ya'yan su domin fahimtar halin da suke ciki.

Daga karshe, Hashim ya hukumar ta su tayi hadin gwiwa da malaman addini da na gargajiya da sauran kungiyoyin matasa domin wayar da kan al'umma kan hatsarin da ke tatare da shan miyagun kwayoyin. Ya kuma ce hukumar ta kafa kungiyoyin wayar da kai a makarantun sakandare 15 da ke jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164