Yanzu-yanzu: Ganduje ya sallami hadiminsa Salihu Tanko Yakasai, Dawisu

Yanzu-yanzu: Ganduje ya sallami hadiminsa Salihu Tanko Yakasai, Dawisu

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya sallami hadiminsa Salihu Tanko Yakasai da ake yi wa lakabi da Dawisu

- Kamar yadda mai taimakawa gwamnan Kano na musamman kan harkokin watsa labarai, Abubakar Aminu Ibrahim ya sanar a Twitter, dakatarwar zai fara aiki nan take

- Gwamnan ya ce ya sallami Dawisu ne saboda cigaba da furta maganganu da suka sha banban da matakin gwamnati da APC da ya ke yiwa aiki game da rashin iya banbance ra'ayinsa da matsayin gwamnati

Gwaman Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sallami mai taimaka masa a bangaren watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu, kamar yadda mai taimakawa gwamnan Kano na musamman kan harkokin watsa labarai, Abubakar Aminu Ibrahim ya sanar a Twitter.

Gwamnan ya ce ya sallami Mr Yakasai ne saboda cigaba da yin maganganu wadanda ba su dace ba da suka sha ban-ban da alkibilar jam'iyyar APC da gwamnatinta da ya ke yi wa aiki.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Baku fi ƙarfin gwamnati na ba, Buhari ya gargaɗi ƴan bindiga

Yanzu-yanzu: Ganduje ya sallami hadiminsa Salihu Tanko Yakasai, Dawisu
Yanzu-yanzu: Ganduje ya sallami hadiminsa Salihu Tanko Yakasai, Dawisu
Asali: UGC

Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano, Mallam Muhammad Garba, wanda ya fitar da sanarwar gwamnan a ranar Asabar, ya ce an sallamar da aka yi wa Dawisu zai fara aiki nan take.

Ya ce hadimin gwamnan ya gaza banbance tsakanin ra'ayinsa ka kashin kansa da kuma matsayar gwamnati a kan batutuwan da suka shafi jama'a da kasa baki daya.

A wani rahoton mai alaka da wannan, hukumar yan sandan farin kaya, SSS, reshen jihar Kano, ta musanta kama Dawisu, saboda kalaman da ya yi na sukar Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC mai mulki, Daily Nigerian ta ruwaito.

Idan za a iya tunawa a yayin da aka sace yaran yan makaranta a jihar Zamfara, Mr Tanko Yakasai wanda ake fi sani da Dawisu, ya shafinsa na Twitter ya bayyana cewa gwamnatin APC ta gaza.

Jim kadan bayan wallafa sakon, an rasa gano inda Yakasai ya ke a cewar abokansa don haka aka fara zargin cewa jami'an yan sandan farar hula na SSS ne suka yi awon gaba da shi.

Mr Alhassan ya ce: "Ba mu kama Salihu ba, ko gayyatarsa ma ba mu yi ba, kada mu kanta shi abokin mu ne, ya kan bamu shawarwari kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro a Kano."

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel