Kano: Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Fahimta a Hukuncin Soke Naɗin Sanusi II

Kano: Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Fahimta a Hukuncin Soke Naɗin Sanusi II

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta soke matakin dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 a ranar 20 ga watan Yuni.

Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya rusa duka matakan da gwamnatin jihar Kano ta ɗauka wajen maido Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.

Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Muhimman abubuwan da ya dave ku sani game da hukuncin shari'ar sarautar Kano Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Facebook

Sai dai akwai muhimman bayanai a cikin hukuncin da ya kamata a ce kun sani, Legit Hausa ta tattaro maku su kamar haka;

1. Kotu ta rusa matakan gwamnatin Kano

A hukuncin da ya yanke, mai shari'a Liman ya soke matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka wajen aiwatar da sabuwar doka.

Kara karanta wannan

"Mutanen Kano ba su goyon bayan rushe sarakuna da maido Sanusi II," Dan'agundi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya maido da Sanusi II ne biyo bayan rattaɓa hannu kan sabuwar dokar masarauta 2024.

Dokar ta kuma rusa masarautu biyar da aka kirkiro ciki har da Mai Martaba Aminu Bayero wanda Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta naɗa.

Bisa tanadin sabuwar dokar, Sarki na 14 Muhammadu Sanusi wanda Ganduje ya tsige a 2020, shi zai koma karagar sarauta da amincewar Gwamna Abba.

2. Ƙorafin da Babba Ɗanagundi ya kai kotu

Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Ɗanagundi ne ya kalubalanci sahihancin sabuwar dokar masarauta ta hannun lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN).

Ɗanagundi ya ɗauki wannan matakin ne domin kare Martabar Aminu Ado to amma a hukuncin da kotu ta yanke, alkali bai haramta dokar masarautun ba.

3. Za a cigaba da shari'ar masarautar Kano

Bugu da ƙari, bayan mai shari'a Liman ya jingine matakan da gwamnatin Kano ta ɗauka a gefe, ya kuma umarci kowane ɓangare su tsaya a matsayinsu na da.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta dauki mataki a shari'ar tsige Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Sai dai tsugune ba ta ƙare ba domin alkalin ya miƙa gundarin shari'ar ga Mai Shari'a Simon Amobeda saboda ƙarin girman da ya samu zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

4. Ma'anar kowa ya tsaya matsayinsa

Abin da kotu take nufi da kowa ya tsaya a matsayinsa shi ne ɓangarorin biyu, wanda ke ƙara da wanda ake ƙara su yi dakon hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

A ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, majalisar dokokin jihar Kano ta yi zargin akwai lauje cikin naɗi a shari'ar, don haka ta garzaya kotun ɗaukaka ƙara.

A rahoton Arise TV, Majallisar ta buƙaci a dakatar da shari'ar da ake yi a Babbar Kotun Tarayya har sai kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci.

5. Waɗanda shari'ar sarautar Kano ta shafa

Baya ga Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II, akwai sauran waɗanda ke cikin wannan shari'a da Babba Ɗan Agundi ya shigar musamman a ɓangare waɗanda ake ƙara.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Babban lauya ya bayyana sahihin Sarkin Kano

A shari'ar, waɗanda ake ƙara sun haɗa da gwamnatin Kano, majalisar dokoki, Antoni-Janar kuma kwamishinan shari'a, da kwamishinan ƴan sanda na jihar.

Sauran su ne Sufeta Janar na ƴan snadan Najeriya (IGP), hukumar tsaron farin kaya (DSS) da hukumar tsaron fararen hula (NSCDC).

Tsagin NNPP ya soki kalaman Kwankwaso

A wani rahoton kun ji cewa tsagin NNPP na Boniface Aniebonam ya nesanta kansa da kalaman Rabiu Kwankwaso kan rigimar sarautar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai a Legas, Aniebonam ya ce NNPP ba ta da alaƙa da zargin gwamnatin tarayya ke rura wutar rikicin Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262