Badaƙalar Emefiele: An Gano Yadda Mutane 4 Suka Kasafta $6.2m da Aka Sata Daga CBN

Badaƙalar Emefiele: An Gano Yadda Mutane 4 Suka Kasafta $6.2m da Aka Sata Daga CBN

  • Wasu takardu da aka gabatarwa babbar kotun birnin tarayya Abuja sun nuna yadda mutane hudu suka kasafta $6.2m na sata
  • Tawagar da shugaban kasa ya kafa domin ta binciki Godwin Emefiele ce ta gano yadda aka sace kudin daga CBN da yadda aka raba su
  • Shugaban sashen gudanar da ayyuka na CBN, Michael Onyeka Ogbu ya ba da shaidar cire kudin da kuma abin da aka ce za ayi da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Takardu sun nuna yadda aka raba dala miliyan 6.2 da ake zargin an sace daga babban bankin Najeriya (CBN) a ranar 8 ga Fabrairu, 2023.

Tawagar da shugaban kasa ya kafa domin ta binciki tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ta yi ikirarin cewa an cire dala miliyan 6.2 daga bankin. da sunan biyan masu sa ido kan zabe.

Kara karanta wannan

Musulmi na murnar Sallah, mazauna Kano na bakin cikin kwace gonakinsu

An sake bankado wata badakalar kudi a lokacin da Emefiele ke gwamnan CBN
Kwamitin shugaban kasa ya gano yadda aka sace $6.2m daga asusun CBN. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Yadda mutum 4 suka kasafta $6.2m a CBN

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa ana zargin jami’an CBN tare da wasu mutane biyu, Adamu Abubakar da Imam Abubakar da sace kudin da kuma kasaftawa tsakaninsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin takardun, masu binciken sun yi ikirarin cewa wani mataimaki na musamman ga Emefiele, Odoh Eric Ocheme ya samu $3.73m daga cikin kudin, yayin da sauran mutanen uku suka raba $2.5m.

Ana zargin Ocheme da cewa ya karbi kaso mafi tsoka daga kudin ne bisa ikirarin zai toshe wasu 'yan matsaloli a cikin babban bankin.

Zargin sace $6.2m daga bankin CBN

Ana tuhumar Emefiele da hannu wajen satar wannan kudin a cikin tuhume-tuhume 20 da hukumar EFCC ta shigar a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja, zargin da ya musanta.

Kara karanta wannan

Aiki da cikawa: Ana tsaka da bikin babbar sallah, sojoji sun kashe dan bindigan da ya addabi Kaduna

A yayin sauraren karar, shugaban sashen gudanar da aiki na ban CBN, Michael Onyeka Ogbu, wanda ke kula da CBN reshen Abuja, ya tabbatar da cire kudin, rahoton Premium Times.

Da yake ba da shaida a shari’ar a ranar 12 ga Fabrairu, Ogbu ya ce ya ba da izinin a cire kudin ne bisa tabbacin cewa mutanen da suka cancanta ne suka ba da izini.

Menene aka yi ikirarin yi da kudin?

Ogbu ya tuna cewa a ranar 8 ga Fabrairu, 2023:

"A ranar na karbi takarda ta bukatar a cire $6,230,000 daga ofishin sashen ayyuka na CBN, kuma takardar na dauke da sa hannun daraktan wannan sashe.
"A cikin takardar, an ce in cire kudin daga wani asusu mai suna Naira Forex Account, kuma za a tura kudin ga wani ma'aikaci a ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
"Hakazalika, takardar ta bayyana cewa ma'aikatar kudi ta tarayya ce za ta dawo mana da kudin a farkon shekarar 2023, bayan an biya masu sa ido kan zabe."

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

Tsohon daraktan CBN ya fallasa Emefiele

A wani labarin, mun ruwaito tsohon daraktan ayyuka na bankin CBN, Ahmed Umar ya fallasa da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya tafka a lokacin canja fasalin takardun Naira.

Ahmed ya shaidawa kotu cewa Emefiele ya canja fasalin Naira a 2022 ba tare da amincewar kwamitin gwamnonin CBN ba, kuma ba yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.