Ocheme: Mutumin da Ake Nema Kan 'Sa Hannun Buhari' Wajen Satar $6.2m a CBN

Ocheme: Mutumin da Ake Nema Kan 'Sa Hannun Buhari' Wajen Satar $6.2m a CBN

  • Odoh Eric Ocheme ake zargi ya yi amfani da sa-hannun Muhammadu Buhari domin a yi barna a babban bankin CBN
  • A lokacin Godwin Emefiele, an yi awon-gaba da $6.2m da aka yi karya da sunan shugaban kasa da sakataren gwamnati
  • Mista Odoh Eric Ocheme yana cikin wadanda ake nema ido rufe, hukuma tana tuhumarsa da hannu wajen satar kudi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Labarin amfani da sa hannun Mai girma Muhammadu Buhari wajen cire kudi daga bankin CBN ya zagaya kusan ko ina.

A wani rahoto da aka fitar, The Cable ta tattaro bayanai ne game da wanda ake zargi da wannan danyen aikin satar sa hannun manya.

Odoh Eric Ocheme
Ana binciken Odoh Eric Ocheme a badakalar CBN Hoto: www.thecable.ng, abacityblog.com, newscontact.com.ng
Asali: UGC

$6.23m sun yi kafa daga bankin CBN

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekara 85 ya shiga hannu a Kano bisa zargin garkuwa da ‘dan Shekara 3

Sa hannun Muhammadu Buhari da Boss Mustapha aka yi amfani da su domin a wawuri $6,230,000 daga babban bankin CBN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fake ne da sunan za a yi amfani da dalolin nan a biya masu lura da zabe a 2023.

Emefiele da Odoh Ocheme a badakalar CBN

Odoh Eric Ocheme na kusa da Godwin Emefiele ne wanda yanzu haka hukumar EFCC tana shari’a da shi a kotu a kan zargin laifuffuka.

An yi ta samun bayanai cewa Odoh Eric Ocheme yana cikin wadanda ake tuhuma a kotu a kan zargin badakalar da aka tafka a CBN.

Kamar yadda ake neman mai dakin tsohon gwamnan bankin CBN, Margaret Emefiele, haka hukuma ke neman Ocheme a duniya.

Wanene Odoh Eric Ocheme?

A watan Mayun 1981 aka haifi Ocheme a garin Makurdi da ke Benuwai, sai ya yi karatun sakandare ne a makarantar cocin ECWA.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan satar $6.2m a CBN da sa hannun Buhari bayan gudanar da bincike

Binciken jaridar ya tabbatar da cewa daga nan ne ya je jami’ar ABU da ke Zariya, ya samu digirin B.Sc a ilmin tsimi da tattalin arziki.

...aikin Odoh Eric Ocheme ban da CBN

Ocheme yana cikin darektocin kamfanonin Ricrem Limited da kuma Beustone Nigeria Limited wanda aka kafa domin aikin gona.

A 2021 hadimin na Emeifle ya auri Chinenyeze Ozioma a wani coci a garin Irete a Owerri a Imo, mutane da-dama sun halarci bikin.

Tsofaffin gwamnoni, ministoci da ‘yan majalisa irinsu Orji Kalu, Alex Otti, Uche Ogah, Jones Onyereri sun halarci wannan babban biki.

Binciken Godwin Emefiele a CBN

Tun a bara Bola Tinubu ya nada Jim Obazee ya binciki abubuwan da suka faru a CBN lokacin da Godwin Emefiele yake gwamna.

Binciken kwamitin Obazee ya shafi Adamu Abubakar, Imam Abubakar da Odoh Eric Ocheme wanda ake nema ruwa a jallo a yau.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar NSCDC ta kama dattijo mai shekaru 85 da laifin garkuwa da karamin yaro

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel