Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya Sun Kwamushe Mutum 18 Bisa Karya Dokar Aikin Hajji

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya Sun Kwamushe Mutum 18 Bisa Karya Dokar Aikin Hajji

  • Hukumomin Saudiyya sun kame wasu mahajjatan bogi da suka shigo kasar ba tare da izinin hukumar cikin gida ba
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ayyukan Hajji a kasar mai tsarki a wannan shekarar
  • Mutane daga sassa daban-daban na duniya na shiga Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji a kowacce shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Kasar Saudiyya - Ma'aikatar Cikin Gida a Saudiyya ta sanar a ranar Juma'a cewa, Rundunar Tsaro ta Hajji ta kama mutane 18 a mashigar birnin Makkah saboda karya dokar Hajji ta hanyar shigo da fasinjoji 91 ba tare da izinin aikin Hajji ba.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya za su tafi maƙwabciyarta domin wanzar da zaman lafiya, an jero dalilai

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya ruwaito cewa an kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis, kuma sun hada da wani daga kasashen GCC, wani bakon haure da kuma ‘yan asalin Saudiyya 16.

An kama mahajjatan bogi a Saudiyya
Yadda aka kama masu aikin hajji ba bisa ka'ida ba | Hoto: Inside Haramain
Asali: Facebook

Hukumar Fasfo ta Kasar ta kaddamar da hukunci ga wadanda aka kamen, wanda ya hada da dauri na tsawon kwanaki 15 ga kowane daga wadanda suka dauko fasinjojin ba tare da izini ba, da kuma tarar SR10,000 (N3,987,003), rahoton Arab News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yaya aka yanke masu wannan hukuncin?

An ninka tarar ne bisa ga adadin mutanen da aka dauka ba tare da izini bag a kowanne mai mota.

Hakazalika, za a kori bakin hauren da suka shigo ba tare da izini ba bayan sun gama zaman gidan kaso daidai da hukuncin da aka yanke masu.

Kara karanta wannan

Super Eagles: Najeriya za ta dauƙo hayar koci daga kasar waje, Finidi George ya gaza

Haka kuma za a fitar da sunayen masu laifin domin a kunyata su a idon duniya kana hukuma ta kwace motocin biyu da aka yi amfani da su wajen safarar mutanen ba tare da takardar izinin aikin Hajji ba.

Ma'aikatar Cikin Gida ta yi kira ga 'yan kasa da baki su bi dokokin Hajji domin a tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali ga dukkan mahajjata yayin gudanar da ibadarsu.

Za a yi hudubar aikin Hajji da Hausa

A wani labarin, rahotanni sun tabbatar da cewa za a fassara hudubar hawan Arafah ta aikin Hajjin bana 2024 zuwa harsuna 20 cikin har da harshen Hausa.

Ana sa ran aKalla mutane biliyan Daya ne a faDin duniya za su saurari huDubar a Hausa da wasu harsuna 19.

Sama da mahajjata miliyan 1.5 daga sassan duniya ne ake sa ran za su taru a dutsen Arafah, wanda ya Kunshi musulmin Najeriya 65,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.