Mutuwar Ɗan Sanda Ta Jawo Tashin Hankali a Abuja, an Ƙona Gawar Wani Ɗan Fashi

Mutuwar Ɗan Sanda Ta Jawo Tashin Hankali a Abuja, an Ƙona Gawar Wani Ɗan Fashi

  • Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja tace an fafata tsakanin jami'an tsaro da 'yan fashi a karamar hukumar Abaji
  • Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, ya ce an yi nasarar kashe 'yan fashi biyu a yayin fafatawar
  • Amma an ruwaito cewa dan sanda daya ya mutu, kuma wasu fusatattun mutane sun kona gawar daya daga cikin 'yan fashin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abaji, Abuja - Wasu mazauna karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja sun kona gawar wani da ake zargin dan fashi da makami ne a ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan fashin sun kai farmaki wani banki a garin da misalin karfe 5:30 na yamma.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta dakume wadanda ake zargi ga kawo tarnaki a tsaron Najeriya

An kashe dan sanda a Abuja
An fafata tsakanin 'yan fashi da 'yan sanda a Abuja, an kona gawar mutum 1. Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Wani jami’in dan sanda ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ‘yan fashin sun fara kai farmaki ofishin ‘yan sanda da ke kan hanyar Toto inda aka harbe wani sufeta mai suna Abila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan fashi sun farmaki 'yan sanda

Ya ce ‘yan fashin da suka shigo yankin a cikin wasu motoci guda biyu da ba su da lamba, sun bude wuta a ofishin ‘yan sandan.

“A gaskiya Allah ne ya kubutar da ni, domin ‘yan fashin na sauka daga motar ne sai suka bude wuta kan ofishin ‘yan sanda.
"A yayin da na yi nasarar tserewa, sai wani sufeto da muka tsere tare ya koma ofishin daga baya saboda sun harbe shi a kirji.”

- In ji dan sandan.

'Yan fashi sun farmaki a Abuja

Legit Hausa ta samu labarin cewa wasu daga cikin ‘yan fashin sun zarce reshen bankin First Bank da ke nesa kadan da ofishin 'yan sandan, inda suka fara harbe-harbe.

Kara karanta wannan

Harajin noma: Ƴan bindiga sun karɓi Naira miliyan 6.2 daga manoman ƙauyukan Kaduna

An ce ‘yan fashin ba su samu nasarar shiga cikin babban dakin ajiyar kudade na bankin ba amma sun yi awon gaba da wasu kudaden da ke a kan kanta.

An kuma ce ‘yan fashin sun fara harbin wani mai gadi ne da ya shiga bandaki na bankin kafin su shiga cikin bankin.

Mutane sun kona gawar dan fashi

An tattaro cewa tawagar hadin guiwar ‘yan sanda, sojoji, ‘yan banga da mafarauta ne suka yi gaggawar zuwa wurin, inda suka fafata da ‘yan fashin, wanda ya kai ga kashe biyu daga cikinsu.

Sai dai an ce wasu fusatattun mutane da ke a wurin sun kama daya daga cikin gawarwakin 'yan fashin sun banka mata wuta.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, wanda ya ce an baza jami’an tsaro a daji domin kama barayin da suka gudu.

'Yan bindiga na karbar harajin noma

Kara karanta wannan

"An maida rai ba komai ba," Atiku ya riga shugaban kasa ta'aziyyar kisan Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun karbi Naira miliyan 6.2 da buhu hudu na shinkafa daga hannun manoman wasu kauyukan Kaduna.

Wani manomi daga yankin ya ce 'yan bindigar sun karbi kudin tare da buhu hudu na shinkafa hudu kafin su yarda su yi noma a gonakin nasu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.