Gungun yan fashi da makami sun kai hari wani Banki, sun hallaka jami’in Dansanda

Gungun yan fashi da makami sun kai hari wani Banki, sun hallaka jami’in Dansanda

- Yan fashi da makami sun kai hari wani banki dake jihar Ekiti

- Jami'in Dansanda guda daya ya mutu, daya kuma ya jikkata

Wasu gungun yan fashi da makami da suka kai farmaki wani banki dake cikin garin Ekiti, sun bindige wasu jami’an Yansanda guda biyu a ranar Alhamis, 19 ga watan Afrilu, inji rahoton jaridar ‘The Nation.’

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a sakamakon harin da yan fashin suka kai, Dansanda guda ya mutu, yayin da dayan yake Asibiti cikin halin rai fakwai mutu fakwai. Wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyarmu cewa yan fashin sun dira bankin ne da misalin karfe 4 na rana.

KU KARANTA: Wani jami’in Dansanda ya rasa ransa a yayin wani hari da yan bindiga suka kai Ofishin Yansanda

Bugu da kari yan fashin sun lalata na’urar bada kudi, ATM, wanda hakan ya sanya jama’a cikin fargaba, suka ranta ana kare, al’amura suka tsaya cak a yankin Ifaki-Ado, Ifaki-Ido da Ifaki-Oyo har na tsawon mintuna 30.

Gungun yan fashi da makami sun kai hari wani Banki, sun hallaka jami’in Dansanda

Harin bankin

Sai dai kwamishinan Yansandan jihar yaki yadda ya bayyana yadda fashin ya kasance, inda yace: “Ban zan iya baku cikakken bayani game harin ba a yanzu, ku saurare mu zuwa wani lokac.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel