Rundunar 'Yan Sanda ta Dakume Wadanda Ake Zargi ga Kawo Tarnaki a Tsaron Najeriya

Rundunar 'Yan Sanda ta Dakume Wadanda Ake Zargi ga Kawo Tarnaki a Tsaron Najeriya

  • Rundunar 'yan sanda a babbar birnin tarayya Abuja ta samu nasarar kama wasu bata-garin 'yan Najeriya da ke sayarwa 'yan ta'adda layukan waya da aka yi wa rajista
  • Wadanda aka kama sun hada da Ndubuisi Okeh, John Jock, Nafiu Tijani, Nasiru Sulaiman, John Njoku, da Suleiman Musa kuma an gano layuka masu rajista da dama a wurinsu
  • Kwamishinan 'yan sanda a Abuja CP Benneth Igweh ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa a nasarorin da su ka samu akwai cafke masu safarar makamai da satar mutane

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta bayyana samun nasara kan wasu miyagu da ke taimakawa ‘yan ta’adda su na muzgunawa al’umaar kasar nan a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Rundunar ta kama matasa shida da ta bayyana sunayensu da Ndubuisi Okeh, John Jock, Nafiu Tijani, Nasiru Sulaiman, John Njoku, da Suleiman Musa a wani samame da ACP Mohammed S. Baba ya jagoranta.

Police
An kama masu sayarwa 'yan ta'adda layukan waya masu rajista Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Vanguard News ta tattaro cewa ana zargin matasan da rashin kishin kasa inda su ke sayarwa ‘yan ta’adda layukan waya da aka riga aka yiwa rajista .

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da aka samu wurin miyagun

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kwato layukan waya masu rajista 1,100 daga hannun wasu matasa shida da ake zargi da sayarwa ‘yan ta’adda layukan ba bisa ka'aida ba.

A wata tattaunawa da manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Benneth Igweh ya ce suna sayar da layukan a kan N3000 zuwa N5000 ga miyagun.

Ya ce wannan danyen aiki na kawo babban cikas wajen yaki da ta’addanci da jami’an tsaro ke yi, kuma ya nuna karara cewa akwai matsala a sashen sadarwar kasar nan, kamar yadda Politics Nigeria ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ɗauki zafi, an dakatar da wasu manyan jiga jigan jam'iyya

A Karin nasarori da su ka samu, CP Igweh ya ce jami’ansu sun yi ram da ‘yan fashi da makami, masu safarar makamai, barayin motoci da masu garkuwa da mutane.

'Yan sanda sun tarwatsa sansanin miyagu

A baya mun kawo muku labarin cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta fattaaki sansanin wasu bata gari a babban birnin tarayya Abuja tare da cafke miyagu hudu.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, Josephine Adeh ta fitar ta ce wadanda aka kama sun hada da Yahaya Abubakar mazaunin Mpape, Mohammed Mohammed, Umar Aliyu da Nura Abdullahi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.