Gungun yan fashi da makami sun kai farmaki wani Banki, sun kashe mutane 2

Gungun yan fashi da makami sun kai farmaki wani Banki, sun kashe mutane 2

Wasu gungun yan fashi da makami sun kai hari a wani Banki dake garin Ilawe-Ekiti na karamar hukumar Ekiti ta kudu masu Yamma, inda suka kashe ma’aikacin bankin da jami’in Dansanda dake tsaron bankin, inji rahoton jaridar The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan fashin sun dira bankin ne da misalin karfe 3 na rana, inda suka bude wuta suna harbin iska, suka tartwasa kofar bankin da nakiya, wanda ya shafi wata mota dake ajiye a kusa da kofar.

KU KARANTA: Rikicin jihar Benuwe: Mataimakin shugaban kasa ya isa Makurdi don ganawa da yan gudun hijira

Daga nan ne fay an fashin suka kutsa kai cikin bankin, inda suka tattara makudan kudade suka yi awon gaba da su. Haka zalika, baya da mutanen da suka kashe, yan fashin sun sanadiyyar samun raunin mutane da dayawa, inda suka kashe sama da awa guda suna tafka ta’asarsu.

Gungun yan fashi da makami sun kai farmaki wani Banki, sun kashe mutane 2
Gungun yan fashi da makami sun kai farmaki wani Banki

Shi ma sarkin garin, Adebanji Alabi ya bayyana kaduwarsa da wannan hari, inda yace yan fashi sun mayar da masarautarsa wajen aikata miyagun laifuka, musamman a yan kwanakin nan, inda yace suna yawan amfani da bamabamai da nakiyoyi.

“Yan fashin sun biyo wata motar banki ce da ta dauko kudi, mun shiga cikin halin tsoro da firgici, abin ya zama tamkar ana yaki, amma mun fara tattaunawa da Yansanda da gwamnanmu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng