Gwamna Lawal Ya Kafa Tarihi, Ma'aikata Za Su Sha Romon Mafi Ƙarancin Albashi Bayan Shekaru

Gwamna Lawal Ya Kafa Tarihi, Ma'aikata Za Su Sha Romon Mafi Ƙarancin Albashi Bayan Shekaru

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince zai fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 daga watan Yuni, 2024
  • Lawal ya sanar da haka yayin ganawa da shugabannin ƙungiyoyin kwadago na jihar Zamfara ranar Laraba, 22 ga watan Mayu
  • Ya ce tun da ya karɓi mulki gwamnatinsa ta aiwatar da tsare-tsare domin tabbatar da walwalar ma'aikata da waɗanda suka yi ritaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara biyan mafi karancin albashi ga ma'aikata daga wata mai zuwa.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu yayin wata ganawa da shugabannin kungiyar kwadago reshen jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: NLC ta sauko daga bukatar N615,000, ta fadi sabon tayi

Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.
Gwamnatin Zamfara za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Mafi karancin albashi zai dawo N30, 000

Premium Times ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce fara biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 a Zamfara ya yi daidai da kudirin Gwamnatin Dauda Lawal na inganta walwala da jin daɗin ma'aikata.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar Zamfara za ta fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 maimakon Naira N7,000 da aka jima ana biya a jihar.

Yaushe Gwamna zai fara biyan albashi?

Da yake jawabi ga shugabannin NLC da TUC, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa ta aiwatar da mafi karancin albashin da nufin zaburar da ma’aikatan Zamfara.

"A yau ina mai sanar da jagororin ƴan kwadago na jihar Zamfara cewa gwamnatina za ta fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 a watan Yuni mai zuwa.

Kara karanta wannan

NAHCON ta faɗi dalilin rashin fara jigilar alhazan Kano da wasu jihohi 6, ta gama da Nasarawa

"Tun lokacin da na hau kujerar gwamnan jihar Zamfara, gwamnatina ta aiwatar da sauye-sauye da dama domin tabbatar da walwalar ma’aikata.
"Mun samu nasarar biyan bashin albashin ma’aikata na watanni uku, biyan kudin hutu, da sauran alawus-alawus. Mun biya kuɗin giratuti ga ma'aikatan jiha da na ƙananan hukumomi da suka ajiye aiki."

- Dauda Lawal.

Ma'aikatan Zamfara za su samu karin albashi

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa na da tsare-tsare da dama ta yadda babu wani ma'aikaci da zai shiga damuwa saboda lokacin ritayarsa ya yi, Daily Trust ta rahoto.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin cimma matsaya da ƙungiyoyin kwadago kan sabon mafi ƙarancin albashi a Najeriya.

An ceto ƴaƴan ɗan majalisar Zamfara

A wani rahoton na daban Ƴan sanda sun kuɓutar da ƴaƴan ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara waɗanda yan bindiga suka sace watanni 17 da suka wuce.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya fadi ainihin lokacin da ya fara mulkin jihar Rivers

Mataimakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda ta ƙasa, CSP Isuku Victor ne ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel